Bilal Villah Ya Kira Ruwa: An Hongoshi a Wani Video Yana Rungumar Wata Yarinya

Shahararren ɗan barkwanci kuma mawaki, Bilal Villah , ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan bayyanar wani bidiyo da ya nuna shi yana rungumar wata yarinya. Wannan bidiyon ya haddasa martani daban-daban daga magoya bayansa da masu bibiyarsa a shafukan sada zumunta. Bilal Villah, wanda aka fi sani da barkwanci da waƙoƙin nishadi, ya shahara sosai a TikTok, Facebook, da Instagram , inda yake jan hankalin mutane da salonsa na raha da zantuka masu ɗaukar hankali. Sai dai wannan bidiyon da ya bayyana ya bar jama’a da tambayoyi da ra’ayoyi mabambanta. A cikin bidiyon, an hango Bilal Villah yana dariya da yarinyar, suna shakatawa tare, sannan a wani lokaci ya rungume ta. Wasu daga cikin magoya bayansa sun kare shi, suna cewa hakan wani ɓangare ne na wasan barkwanci ko kuma nishadi kawai. Sai dai wasu sun yi Allah-wadai da hakan, suna ganin bai dace ba, musamman ga mutum mai tasiri irin shi. Wannan shine bidiyon; Bayan bayyanar bidiyon, wasu sun yi hasashen cewa hakan wat...