Rigimar taci gaba da daukan zafin inda hadiza kabara ta mayarda martani
Tun kwanakin baya ake ta dauki ba dadi da musayar nyawu tsakanin jaruma hadiza kabara da kuma Rashida mai sa'a, inda hadiza kabaran tayi gugan zana akan tsohuwar matar g fresh al ameen da kuma Rashida mai sa'a, inda ta kirasu da yan wahala a wani faifan bidiyo dake yawo a tiktok
Ta bangaren Rashida mai sa'a yaran gidanta da abokanan ta sukai ta mayarda martani sai dai duk abunda suke fada jaruma hadiza kabara bata taba mayarda martani ba sai wannan karon kamar yadda zaku gani a video nan.
Jarumar tace duk wacce ta isa bata jin magana tazo har inda take ta takaleta taga yadda ake yi, duk soki burutsun da sukeyi na haukar banza ne, tunda mutum baxai iya zuwa har inda take ba yayi mata rashin kunya
Lamarin yaci gaba da yamutsa hazo inda jama'a da yawa sun tofa Albarkacin bakin su, sai dai dayawa sun fi ganin laifin Rashida mai sa'a inda suke fadin ai ta damfari jama'a dayawa kuma itace silar fasa auren G fresh da alpha charles.
Comments
Post a Comment