Ali nuhu ya boyewa duniya asalin sa, kannywood news ta bankado wasu abubuwa game da jarumin
Ali Nuhu, fitaccen jarumin fina-finan Hausa da Nollywood, yana daya daga cikin shahararrun mutane a Najeriya, musamman a cikin masana'antar Kannywood. Duk da haka, akwai tambayoyi da dama game da asalin sa da kuma bayanan da yake bayarwa game da inda ya fito. Bincike ya nuna cewa Ali Nuhu ya sha bayyana kansa a matsayin haifaffen garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, amma mahaifinsa, Alhaji Nuhu Poloma, asalinsa dan garin Gelengu ne, wani kauye a karamar hukumar Balanga, jihar Gombe. Wannan yana nuni da cewa Ali Nuhu na da asali daga jihar Gombe, ba wai Borno kawai ba kamar yadda ya saba fada wa duniya.
Da Kuma Barrister Samuel (Samaila) Nuhu Poloma wanda shima kuke gani a hoto na kasa.
Sai kuma kanwarshi Hauwa Nuhu Poloma obadan wacce kuke gani a hoto.
Sai na karshe Aisha wanda akafi sani da indo nuhu poloma ga hoton ta a kasa.
Wadannan ‘yan uwan nashi suna da nasu tasirin a cikin al'umma, musamman a jihar Gombe, amma ba a taba ganin Ali Nuhu yana magana game da su ba a bainar jama'a, mutane masu capacity da kuma kima a jahar Gombe kasancewarsu yan siyasa wayanda ake damawa dasu dan acikin su Kabiru (copa) yayi dan majalisa, shi kuwa samaila nuhu polama babban ma'aikacine a hukumar zabe kuma babban barrister.
Ali Nuhu ya sha bayyana kansa a matsayin cikakken Bahaushe, amma asali yana da dangantaka da kabilar Waja, daya daga cikin kananan kabilu da ke jihar Gombe kasancewar mahaifinshi dan kabilar waja ne, wanda hatta kaninshi yanada sarauta a masarautar waja.
Waja na da yaren sa wanda yake da bambanci da Hausa, amma ba a taba jin Ali Nuhu yana magana ko kuma yana magana akan wannan yaren na Waja ba. Wannan ya sa wasu ke ganin kamar yana boye asalin sa don a gan shi a matsayin cikakken Bahaushe.
Dalilin boye wasu daga cikin wadannan bayanai na iya zama na sirri ko kuma na yanayi. Wata kila Ali Nuhu yana son kare kansa daga matsaloli ko tambayoyi da ka iya tasowa daga al'umma. A wani bangaren kuma, yana iya zama ra'ayin mutum kawai na mayar da hankali kan abin da ya fi muhimmanci ga rayuwarsa da aikinsa.
Ali Nuhu, babu shakka, ya kafa sunan sa a matsayin daya daga cikin manyan jarumai a masana'antar fina-finan Najeriya. Duk da haka, tambayoyi game da asalin sa, dangantakar sa da ‘yan uwansa, da kuma dalilin boye wasu bayanai na ci gaba da kasancewa abin magana. Ko da ya ke, yana da muhimmanci a gane cewa kowane mutum yana da ‘yancin yanke shawara kan abin da zai bayyana game da rayuwarsa da na danginsa.
Comments
Post a Comment