Jarumin Kannywood Garzali Miko ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

 


Shahararren jarumin Kannywood, Garzali Miko, ya bayyana ra’ayinsa kan wani jawabi da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda ya ja hankalin al’umma a kafafen sada zumunta. Buhari ya yi magana kan gidajen haya mallakarsa, wanda ya haifar da martani daga mutane daban-daban, ciki har da Garzali.

A cikin wani posting da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Garzali ya nuna takaicinsa kan jawabin tsohon shugaban kasa, yana mai cewa, “Buhari, ka fa daina damunmu fa! Ka barmu da abunda yake damunmu.” Wannan tsokaci ya fito daga bakin jarumin cikin yanayi na fushi, yana nuni da cewa akwai matsalolin da suka fi wannan muhimmanci da ya kamata a mayar da hankali akansu. Ga bidiyon da yayi jawabi akai


Garzali ya kara da cewa a halin da ake ciki, jama’a na fama da matsaloli masu tsanani, musamman rashin tsaro, tattalin arziki mai rauni, da kuma hauhawar fiarashin kayayyaki. Saboda haka, ya ce tsohon shugaban kasa ya kamata ya fi damuwa da wadannan matsaloli fiye da bayyana kadarorin kansa.

Martanin Garzali ya jawo hankulan mutane da dama a kafafen sada zumunta. Wasu sun yaba masa da yadda ya bayyana gaskiyar ra’ayinsa a fili, yayin da wasu suka yi suka, suna ganin bai dace ba ya fadi haka kan tsohon shugaban kasa. Duk da haka, tsokacin jarumin ya kara fito da ra’ayoyin jama’a kan halin da kasa ke ciki da bukatar shugabanni su maida hankali kan inganta rayuwar al’umma. Ga bidiyon da yayi bayani akai


Comments

Popular posts from this blog

Ali nuhu ya boyewa duniya asalin sa, kannywood news ta bankado wasu abubuwa game da jarumin