Shin Da Gaske Ne Anyiwa Hamisu Breaker Asiri Kwanakin Baya? Kannywood News Ta Binciko gaskiya

 

A kwanakin baya, wani labari ya fara yawo a kafafen sada zumunta da ke nuni da cewa mawakin soyayya Hamisu Breaker an yi masa asiri, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masoyansa da mabiyansa. Wannan zancen ya dauki hankalin mutane sosai, musamman ma wadanda ke bibiyar al'amuran fina-finan Hausa da Kannywood.


Sai dai binciken da Kannywood News ta gudanar ya tabbatar da cewa wannan labari ba shi da tushe balle makama. Cikin wani jawabi da jaridar ta fitar, ta bayyana cewa ba wata shaida ko hujja da ke nuna cewa an yiwa Hamisu Breaker asiri. Abin da ya faru kawai shi ne mawakin ya yi rashin lafiya, wanda ya saba faruwa saboda yana fama da cutar typhoid tun can baya.


Rahotannin sun bayyana cewa Hamisu Breaker yana yawan fama da wannan cuta, wadda take shafar jikinsa sosai har ma ta kai ga likitoci sun shawarce shi da ya daina shan ruwan randa, sai dai ya rika amfani da ruwan roba kawai. Wannan matsala ce ta sanya idan aka duba idon mawakin, za a ga sun yi ja, alamar da ta saba kasancewa a wajen masu fama da typhoid. Wannan ya sa wasu ke tunanin ko asiri ne aka yi masa, amma wannan zance babu gaskiya a cikinsa.


[Ads: Kalli sabon video Hamisu Breaker mai jan hankali(zaku iya shiga videon da farko su sako muku talla, idan baiyi ba ku sake dannawa a karo na biyu zaiyi insha Allahu)]

Kannywood News ta kara da cewa irin wannan jita-jita ba su dace ba, domin suna iya haifar da fargaba ko kuma zubar da mutunci. Ta shawarci mutane da su daina yada labaran da ba su tabbata ba, kuma su rika neman gaskiyar al’amura kafin su yada su a kafafen sada zumunta.

A karshe, Hamisu Breaker yana samun kulawar likitoci, kuma yana kan hanyarsa ta warkewa daga rashin lafiyar. Masoyansa da mabiyansa sun bukaci a ci gaba da yi masa addu’a domin samun lafiya da kuma cigaban aikinsa na waka.

Comments

Popular posts from this blog

Ali nuhu ya boyewa duniya asalin sa, kannywood news ta bankado wasu abubuwa game da jarumin