Wakokin Kannywood na da cike suke da batsa in ji Aliyu dahiru Aliyu (Sufi)
Wani shahararren mai amfani da kafar sada zumunta Aliyu dahiru Aliyu (sufi) ya bayyana cewa duk tsoffin Wakokin kannywood cike suke da batsa, inda yayi karin bayani yace;
Wato wakokin Kannywood na da cike suke da batsa amma da yake mutane hankalinsu ba ya kai ba ma sa ganewa.
Yanzu nake fahimtar me Abubakar Sani yake cewa a wakar Bajinta. Duk shekarun da na yi ban gane ba sai yau!
Jiki da zafi taho ka tausa
Ka tofa yawunka za na lasa
Mu sha kida mu yi rawar makosa
Zan yo ma juyin so ko a filin Nagoma
Bacci na tashi magagi a fuska
Ka tashi bacci mu fara harka
Harkar yabo ko ko za mu leka
Dukkan harka riba za ka so in ka koma.
Da Ado Gwanja ya yi rabin wannan da tuni yana ofishin Hisbah.
Shin ya kuke ganin bayanin nasa?
Comments
Post a Comment