Yan sanda sun kama wani malami saboda yayi addu'a bata karbu ba.
Yan sanda sun kama wani malami saboda yayi addu'a bata karbu ba.
Yan Sandan Area Command Na Manumfashi dake Jahar Katsina, Gaskiya Baku Kyautawa Wannan Malamin da kuka Dauko shi Tun daga Maiduguri zuwa katsina akan Zargin Addu'ar da yayi Bata Karbu ba!
Yakamata Mutumin da yakawo muku karar cewa Wani Malami dake Maiduguri ya karbi kudin shi akan Rokon Allah! Kuma wai Rokon Allah baiyyi Aiki ba, kamata yayi kusan cewa wannan ba criminal offense bane, kusan cewa is a Civil Contract tsakaninsu. Which is purely civil case! Babu Tursasawa, Ba damfara ba, Ba kwace yayi da karfi ba, ba Duka babu zagi, Haba ?
Na Farko,Rokon Allah, kowa ya san, Abu ne wanda ba ganinshi ake a zahiri ba, Kuma Bashi da Lokacin da za'ace An karbe shi ko akasin haka. MAI Bayar da Kudin da MAI Karban Kudin Rokon Allah duk sun san kar Harkar, sun san Yadda Abun yake!
Idan Ba ZaLinci Yan Sanda Area Command na Manumfashi, da rashin iya Aiki, daRashin Sanin Darajan Hakkin mutum, da Karancin Sanin Doka, da Kasa Banbance Tsakanin Laifi da ba Laifi ba.
Tayaya zaku Je Har Maiduguri, a Irin wannan zargin Laifin, Ku Dauko mutum kamar Wani Buhun Wake. Ku Ajiye shi sama da Kwana Goma (10 days) a cell, duk da Kun Tilas mishi da biyan Million Daya .
Daga baya kuka Kaishi Kotu, Kuka Tilasata mishi idan Bai mayar da sauran Kudin Ba. Zaku Aika shi Gidan Yari. Yanzu haka yana Gidan Yari.
Wannan Babban ZALINCI ne , Yanzu ko an bada Belinshi, Tayaya zai samu Wanda zai tsaya mishi a Mulumfashi? Yanzu menene Riban Zalincin nan? Abunda aka baku Na Tabbata yanzu ya kare!
Kun Rabashi da Iyalensa, Kun Dauko shi tun daga wani Gari kun kawoshi Malunfashi , Kastina State, Saboda kawai kuna Gadaran kuna da Iko a wajen, Akan laifin da bai dace ace Yan Sanda sun saka bakinsu ba.
Haryanzu Malamin yana Tsare a Gidan Yari a Kastina!
Gaskiya Yan sandan Area Command na Manufumshi, Kun ZALINCI Bawan Allah. Kuma ku tuna Allah yana Kallonku.
Ga Bandits kuna Kallonsu anma kun iya zuwa har Maiduguri ku dauko mutum, ku tsare shi , ku Aikashi Gidan Yari akan Zargin da ba laifi bane a fuskar Doka!

Comments
Post a Comment