Mr Bangis Ya Zargi Adam A Zango Da Amfani Da Basirar Sa Wajen Gina White House Family
Fitaccen mawaki kuma dan rawa na Kannywood, Mr Bangis, ya tayar da kura a dandalin sada zumunta bayan da ya fito fili ya zargi kamfanin White House Family — karkashin jagorancin jarumi Adam A Zango — da amfani da fasaharsa ta waka da rawa domin cika burinsu, ba tare da bashi kulawa ko bayyanawa ga duniya yadda ya dace ba.
A cikin wani rubutu mai cike da zafin rai da tunani a shafin Facebook dinsa, Mr Bangis ya bayyana damuwarsa da cewa:
"Wani irin record label za ace an dauke ka kusan 8 years amma ba a taba sanin inda ka fito ba, sai White House Family sunyi anfani dani gurin cin ma burinsu — especially a part of music part and dancing part."
Kamar yadda kuke gani a screenshot.
Wannan kalami ya haifar da zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta, inda magoya baya da dama suka bayyana tausayinsu ga Mr Bangis, yayin da wasu ke bayyana mamakinsu kan yadda aka iya amfani da fasahar mutum tsawon lokaci ba tare da bashi cikakken kulawa ko daukaka ba.
Mr Bangis dai yana daga cikin matasan da suka dade suna taka rawar gani a bangaren waka da rawa a Kannywood, musamman wajen kirkira da tafiyar da sabbin salon rawa da aka saba gani a bidiyon wakokin White House Family.
Sai dai har yanzu, Adam A Zango da kamfaninsa na White House Family ba su fitar da wata sanarwa ko martani game da zargin da Mr Bangis ya yi ba, lamarin da ke kara janyo hankalin jama’a da sa ido kan wannan batu.
Masu fashin baki kan harkar fina-finai da waka na ganin wannan sabani wata hanya ce da ke sake fito da irin kalubalen da matasa ke fuskanta a masana'antar nishadi, inda galibi suna taimakawa wajen gina manyan sunaye ba tare da samun hakkinsu yadda ya dace ba.
Ko dai wannan zargi zai bude sabon babi a rayuwar Mr Bangis, ko kuwa shiru ne zai rufe lamarin — lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.
Comments
Post a Comment