Halin da mansura isa take ciki a yanzu

 


Jaruma mansura isa ta bayyana halin da take ciki.

Jarumar dai ta koka kan yadda wasu daga cikin gurbatattun mutane suke kokarin ganin sun durkusar da ita sun mayar da ita baya ta hanyar sakata asara akan wani film dinta fa taski mai suna faliha da falisha.

Inda wasu da ga cikin YouTubers ko ince blogger suke daukan wani sashi daga cikin fina finan nata suke daurawa a shafin su wanda hakan yana rage mata makallata kuma hakan asara yake jawo mata kamar yadda tayi bayi a cikin wannan hoton dake kasa.


Jarumar tayi Allah wadai da kuma tabbatar wa da duniya cewa zata dauki mummunan mataki akan duk wanda yake sace mata film yana daurawa akan shafin sa zatayi shara'a da kowa kuma sai taga gatan mutum ko wanene shi.
Bata tsaya anan ba jarumar ta kara dace kada wani jarumi ko jaruma ya bata hakuri duk sanda ta dauki mummunan mataki akan mutum tunda tun farko tayi sanarwa

Ta bangaren abubakar bashir mai shadda da hajiya fauziya d sulaiman sun bata shawararwarin yadda zata yi maganin duk wani dake daukan kayan ta kamar dai yadda sukayiwa film din garwashi


Comments