Yadda jarumi hamza yahya ya koka da yan kannywood.
Jarumi hamza yahya yana daya daga cikin fitattun jaruman kannywood wanda taurarawarshi ta fara haska wa a masana’antar Kannywood sai dai daga baya wata jarrabawar ta afka masa inda yayi hadari wanda har sai da yakai anyi masa gyaran hamci, wannan sanadiyar ne ya janyo jarumin ya soma baya baya da masana’antar.
sai dai a yan kwanakin nan jarumin ya koka a kan yadda jaruman kannywood suka manta dashi kuma suka daina tuntubar shi a duk wani abu daya taso nasu.
Kamar yadda ya bayyana a shafin sa na sada zumunta na Instagram jarumin yace "yanzu fa an daina gayyatarshi duk wani taro da ake gabatarwa na kannywood"
Sannan kwana kwanan nan anyi rabon kayan abinci amma babu wanda ya tuntube shi domin ya bashi koda kwallin shinkafa daya ne.
Hakan yasa jarumin ya koka sosai sai dai babu daya daga cikin yan uwanshi jarumai da ya goyi da bayanshi kowa ya yi buris da lamarin shi.
Comments
Post a Comment