Shin ko Ali Nuhu ya kyautawa Kannywood kuwa, A wajen taron Masu bautar kasa (NYSC) da akayi a jihar plateu
A wani taro da aka gabatar a jahar Plateau wanda ya samu halartar jarumi kuma uba ga duk wani dan Kannywood ali nuhu, sai dai taron ya janyo cece-kuce kwarai da gaske ganin yadda jarumin ya kasa bayyana kanshi a matsayin jarumin kannywood.
Jarumin yayi maganganu da dama kuma yayi jawabi sosai akan hanyoyin da za'a bi a tallafawa matasa su shigo harkar film, sai dai a bayanan nashi jarumin ya kasa ambatar kannywood sai dai Nollywood inda yake ta karfafawa matasan gwiwar ganin yadda zasu shigo masanaantar Nollywood ba kannywood.
Hakan ya jawo maganganu da yawa a dandalin sada zumunta na X wanda aka fi sani da twitter, mafi yawa sun bayyana takaicin su ganin yadda jarumin ya wofantar da asalin sa, wasu ma cewa sukayi jarumin yana kunyar ambatar kannywood din ne saboda yasan babu wani abun azo a gani a masana’antar.
Haka a shafin sa na sada zumunta na Instagram jarumin ya sake magana akan batun inda wasu sukayi caaa akan Meyasa baya ambaton kannywood a duk wani taron da yake zuwa sai dai Nollywood kamar yadda kuke gani a hoto jarumin ya kasa ambaton kannywood.
Nan kuma wasu daga cikin masu korafi ne yayi magana
Bayan kuma jahar Plateau tafi kusa da kannywood akan Nollywood
Shin minene ra'ayinku akan hakan?
Comments
Post a Comment