Rigima Ta Kara Karfi Tsakanin Sayyada Sadiya Haruna da Jaruma Rashida Mai Sa’a
Rigimar da ta barke tsakanin Sayyada Sadiya Haruna da jaruma Rashida Mai Sa’a ta dauki sabon salo, inda ake zargin cewa Rashida ta cinye kudaden ankon bikin G Fresh Al Ameen.
Sayyada Sadiya Haruna ta fito fili tana zargin Rashida Mai Sa’a da rashin gaskiya a batun kudaden, tana cewa mutane sun biya kudi don anko amma ba a ga kaya ba. Rashida, a nata bangaren, ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta aikata wani abu da ba daidai ba.
Kamar yadda kuke gani a bidiyo:
Magana na ci gaba da daukar hankali a kafafen sada zumunta, inda mabiyan su ke tofa albarkacin baki, wasu na goyon bayan Sayyada Sadiya, yayin da wasu ke kare Rashida Mai Sa’a.
Ana jiran ganin yadda rikicin zai kaya, yayin da masu ruwa da tsaki ke kokarin warware matsalar.
Comments
Post a Comment