Menene makomar wayan nan Mawakan A shekaran 2025

Mun gudanar da bincike mai zurfi akan wasu mawakan Hausa yanayin trending din su da kuma makomarsu a wannan shekarar


Dayawa suna mamakin yadda mawakan suka daina trending lokaci daya kuma aka daina jin su sosai bayan dayawa daga cikin yan uwansu da suka taso tare masana’antar tana tafiya dasu har yanzu.

Binciken mu ya takaita ne akan dalilan da ya saka mawakan suka daina tashe lokaci daya


1. Husainin danko:

A iya binciken mu mun gano wasu kurakurai da mawakin ya dinga tafkawa wanda hakan sun taka muhimmiyar  wajen rashin ci gaba da tashe, kowa ya sani cewa hussaini danko mawaki ne wanda ya karbu sosai musamman a gidajen gala da kuma taron biki, sai dai lokacin da mawakin yake tashen sa, ya kasa tsayawa ya inganta tafiyar shi ta hanyar yin video album da sauran su, yana daya daga cikin kuskuren da ya tafka shine yadda ya bari wasu suke hawa wakokinshi barkete hakan ya jawo da yawa basa iya gane shi, kuma ya kasa yin hadin gwiwa da sauran manyan mawaka da furodusoshi na zamanin shi, rashin samun promotion da kuma banning dinshi da akayi a Instagram ya jawo masa ci baya sosai.


2. Abubakar Sani:

Da yawa daga cikin abokan sana'ar shi sun tabbatar mana da cewa Abubakar Sani shi ya kashe kanshi da kanshi, lokacin da yake kan sharafin shi baya bawa masoyanshi lokaci su hadu ko su tattauna dashi, wanda mun samu labarin cewa hatta mahaifin shi sai yayi da kyar yake samun ya hadu dashi sai ya tabin wasu kamun yake ganin shi, kuma a lokacin shi ya kasa kyautata mu'amala mu'amalarshi da abokan sana'ar shi wanda a yanzu suma suka fita daga lamarin shi

Wannan ya jawo wa mawakin ci baya sosai.


3. Garzali miko:

Mawakin ya samu cikas tun bayan da masoyan shi suka gano salon da yake amfani dashi a waka salo daya ne, bayan kowa ya sani mutane a koda yaushe suna tsammanin samun wani abu sabo daga gwarzo su, saboda haka rashin updating ya kashe kariyar garzali miko sosai, bayan haka masoyan shi suna korafin bai iya magana ba, kuma baya taba barin a dauki hoto dashi sosai, wanda ni a gaba na anyi haka sai dai muce Allah ya kyauta.


4. Sadi sidi Sharifai:

Ba kamar sauran mawaka da muka lissafo a sama ba mawaki sadi sidi sharifai lamarin daukaka shi da sauki, saboda ko yau yayi waka za'a saurare shi, sai dai matsalar shi rashin amfani da zamani, kamar sauran yan uwanshi, Ali jita, nazifi asnanic, su suna amfani da zamani kuma suna shirya fina-finai wanda a film din suke saka Wakokin su, a takaice dai rashin sanin salon promotion shi ya kashe mawakin kwarai da gaske.


#kannywoodNews 



Comments

Popular posts from this blog

Ali nuhu ya boyewa duniya asalin sa, kannywood news ta bankado wasu abubuwa game da jarumin