Mabiya Darikar Tijjaniyya Sun Yi Wa Dan Wasan Barkwanci "Mazaje" Kaca-Kaca Kan Zagin Shehunan Su
A kwanakin nan, wata gagarumar cece-kuce ta barke a kafafen sada zumunta sakamakon yadda mabiya darikar Tijjaniyya suka yi wa dan wasan barkwanci da aka fi sani da "Mazaje" kaca-kaca. Hakan ya faru ne bayan zargin cewa yana furta kalaman batanci da cin zarafi ga mashahuran shehunan darikar.
A cewar wasu mabiya darikar Tijjaniyya, Mazaje ya yi amfani da hanyoyin barkwanci wajen sukar shugabannin su, musamman manyan shehunan da suke girmamawa. Wannan abu ya haifar da bacin rai ga mabiyan darikar, wanda hakan yasa suka caccake shi ta kafafen sada zumunta da kuma bukatar ya janye kalamansa.
[TIRKASHI]: Fina-Finan Kannywood Sun Zama 'Yan Talla na Lalata—Malaman Addini Sun Yi Kira Da A Dakatar Da Wasu! Karanta cikakken labarin anan https://tinyurl.com/Tarbiyya-a-Kannywood
Wasu daga cikin mabiyan darikar sun bayyana cewa, addini da shugabanninsa ba su dace da barkwanci ko cin mutunci ba. Sun bayyana cewa suna mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, amma ba tare da cin zarafin wasu ko muzantawa ba. Har wa yau, sun nemi Mazaje da ya fito ya bayar da hakuri ga mabiyan darikar domin kwantar da wutar rikicin da ke neman yin kamari.
A daya bangaren kuma, wasu daga cikin masoyan Mazaje sun kare shi da cewa yana yin barkwanci ne kawai ba tare da wata manufa ta cin zarafi ba. Sun bayyana cewa bai kamata a dauki dukkan maganganunsa da muhimmanci fiye da yadda ake daukar wasan barkwanci ba. Amma duk da haka, da dama daga cikin jama’a sun bukaci da a dinga kula da iyaka tsakanin barkwanci da cin mutunci, musamman idan ya shafi addini da shugabanninsa.
Tuni dai wannan lamari ya ja hankalin jama’a da dama, inda wasu ke ganin ya kamata ‘yan wasan barkwanci su kasance masu lura da kalaman da suke furtawa domin guje wa tada husuma a tsakanin al’umma. Yanzu dai ana jiran ganin ko Mazaje zai yi martani kan wannan zargi ko kuma ya dauki matakin da zai shawo kan rikicin da ya barke.
Comments
Post a Comment