Dukan da akayiwa Y-amerika yayi kadan inji Samha M Inuwa
Jaruma ta kara da cewa "Wallahi Y Amerika Bai Daku Ba, Ina Kokarin Ba Shi Shawara Ya Daina Maganar Batsa da maganganun da Yake Yi a Tik-tok Saboda Wata Rana ko ba komai wata rana zai Ka Haifa Amma Ya Ce Shi Yanzu Ma Ya Fara"
Martanin Y-Amerika "ba karamin yaro bane da zaki ba ni shawara."
Bayan jayayya ta yan mintuna a tsakaninsu a yayin da ake hirar Live a sabon shafin na Tik-tok Samha ta tambayi Y. Amerika ko akwai wani buri yake so ya cimmawa kafin ya daina wannan badalar da yake yi a Tik-tok.
Nan take ya bayyana mata cewa lallai yana da burin da yake son cimmawa, wanda jin hakan ya sa ta nemi ya tura mata lambarsa domin ta kira shi su karkare magana.
Y Amerika ya yi wa Samha alkawarin cewa matukar ta biya masa bukatunsa, shi kuma ya yi alkawarin zai daina abinda yake yi a tìktok.
Comments
Post a Comment