Anyi kaca kaca tsakin Jaruman Kannywood Samha M Inuwa da Jaruma Maryam Kk, Wanda ya jawo tone tonen Asiri.

Wani lamari afku tun jiya a dandalin sada zumunta na Tik-tok inda aka hango wasu daga cikin jaruman kannywood suna ta zage zage da tona asirin junan su, sai dai jama'a sun tabbatar da cewa jaruma samha m inuwa ita ta fara futowa tana zagin Jaruma Maryam kk akan tana zargin ta akan tana mu'amala da saurayinta wanda har gift yake bata ita ma take bashi kamar yadda zaku gani a bidiyon nan na kasa;


Bayan futan wannan bidiyon da jaruma samha m inuwa tayi shine itama jaruma Maryam kk aka hangota tana mayarda martani inda take cewa tunda take tareda samha m inuwa ta fahimci munafuka ce, saboda ta taba shiga mata fada da sukayi da jaruma Aisha humaira amma daga karshe itace ta fara nunawa Aisha humaira gidanta folisawa suka kamata kamar yadda zaku gani a video na kasa.


Daga bisani kuma sai rigimar ya kwace ya zama tsakanin kewayen samha da kewayen kk inda dukan su suka dau alwashin babu zaman lafiya tsakanin su kamar yadda kuke gani a bidiyo na kasa

Al amarin ya dagula lissafin kowa inda ake ganin yadda jaruman suke da junan su ba a taba jin kansu ba sai gashi yau sun futo suna zage zage da cin mutuncin juna.


Comments

Popular posts from this blog

Ali nuhu ya boyewa duniya asalin sa, kannywood news ta bankado wasu abubuwa game da jarumin