Malamai sunyi ca akan Jarumi Adam A Zango
Tun bayan bullar wani bidiyo da jarumin yayi a karkashin daukar nauyin jaruma Rahama Sadau, malamai sunyi ta tofa albarkacin bakinsu inda sukayi kira ga jarumin akan shigar da yayi na alkyabba
Kamar yadda kuke gani a wannan bidiyon
Malamai da dama sunyi ta bayanai kowa da fahimtar sa sai dai mafi akasarin su sun bayyana cewa jarumin bai kyauta ba wani ma cewa yayi jarumin yayi ridda, saboda Ba'a wasa da addini
Inda wasu kuma sukayi tsokaci akan maganganun malaman inda suke nuna cewa lallai hassada kawai ake yiwa jarumin saboda bashi kadai bane ya fara futowa a film da alkyabba ko a wakaba
Sai dai ta bangaren jarumin baice komai ba, kawai yaci gaba ne da harkokin shi kamar yadda ya saba
Allah yasa mu dace ameen
Comments
Post a Comment