Ali Nuhu, fitaccen jarumin fina-finan Hausa da Nollywood, yana daya daga cikin shahararrun mutane a Najeriya, musamman a cikin masana'antar Kannywood. Duk da haka, akwai tambayoyi da dama game da asalin sa da kuma bayanan da yake bayarwa game da inda ya fito. Bincike ya nuna cewa Ali Nuhu ya sha bayyana kansa a matsayin haifaffen garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, amma mahaifinsa, Alhaji Nuhu Poloma, asalinsa dan garin Gelengu ne, wani kauye a karamar hukumar Balanga, jihar Gombe. Wannan yana nuni da cewa Ali Nuhu na da asali daga jihar Gombe, ba wai Borno kawai ba kamar yadda ya saba fada wa duniya. Alhaji Nuhu Poloma, mahaifin Ali Nuhu, ya kasance mutum mai tasiri a harkar siyasa a yankin Gombe. Shi ne ya kafa harsashin rayuwar Ali Nuhu, wanda ya gina kansa a matsayin jarumi mai farin jini. Duk da haka, ba kasafai Ali Nuhu yake magana akan mahaifinsa ko dangantakar sa da shi ba, wanda hakan ya bar mutane da tambayoyi kan dalilin wannan boye-boye. Daya daga cikin ...
Comments
Post a Comment