Alhakin wasu shi ya kashe kasuwar Kannywood a idon duniya - Binciken Kannywood News
Tun ba yau ba tun farko farkon fara kafuwar masana’antar Kannywood an sha samun korafi akan yadda ake daukan alhaki da kuma kashin dankali a masana’antar Kannywood, a wancan lokacin furodusoshi da daraktoci sun wulakanta kananan jarumai bila adadin wanda hakan ya jawo rashin tausayi da kuma rashin imani ga duk jarumin da ya samu dama ya wuce kadamin fafutukar neman samun waje.
A masana’antar Kannywood ana yin wani abu mai kama da cin zali da kuma nuna kabilanci wanda shekaru dayawa ana haka kuma har yanzu ba'a samu canji ba, dan karamin misali mu dauki jaruman jos, wanda har yanzu furodusoshi da daraktoci dake Kano ke nuna musu wariya a matsayin su na yayan Kannywood.
[TIRKASHI]: Anyi kaca kaca tsakin Jaruman Kannywood Samha M Inuwa da Jaruma Maryam Kk, Wanda ya jawo tone tonen Asiri. Karanta cikakken labarin anan https://tinyurl.com/Samha-m-inuwa-Maryam-kk
Shiyasa suma idan suka samu dama basa tausayawa wani producer idan ya shiga wani hali, kamar abunda ya faru da darakta ashiru na goma da sauran jaruman!
Kwana kwanan zuwan social media da sauran kafa ta sada zumunta ya dakile kana ya kashe kasuwar Kannywood sosai da kaso 60 wanda hakan babban barazanace ga furodusoshin da kuma daraktocin, Akwai yara da yawa wayanda ba yan kannywood bane amma sanadiyyar social media sun sanu sannan sun samu kudi kuma basa bukatar taimakon wani jarumi ko furodusa dan ya taimaka musu, wanda yanzu haka wasu daga cikin jaruman namu sun jefar da sabgar Kannywood din sun rungumi tiktok shiyasa koda an kore su daga masana’antar basa jin komai.
Zuwan wannan social median nafi tunanin alhaki ne na kananan jarumai da aka dauka can baya, wasu jaruman an dake su, wasu an zagesu an ci mutuncin su, kai wasun su ma anki a biyasu hakkin su na aikin da suka yi, kuma duk inda zalunci yayi yawa dole ne a samu ci baya da kuma sakayya daga Ubangiji.
Albishiri ku
Zaku iya bamu tallan ku domin mu daura muku akan shafin mu na website da kuma Facebook inda dubban nin mutane suke ganin abubuwan mu ta wannan hanyar zaku iya samun kwastomomi sosai, zaku iya tuntubar mu ta wannan layin ta Whatsapp kawai 08149299509
Ku duba yadda tiktokers irin su bilal villah, king kabeer, ngulde, Arab da sauran su suke tasowa ba tare da taimakon wani furodusan ba, muna kira da a gyara sai a ga chanji
Comments
Post a Comment