Mawaki Garzali Miko Ya Caccaki Abokan Sana'arsa, Inda Yace Basu Son Masoyansu Sai Bare
Mawakin nan shahararre Garzali Miko ya tada kura a masana’antar Kannywood bayan wani posting din da ya yi inda ya zargi wasu abokan sana’arsa da rashin son masoyansu na gida, suna fifita mutanen waje fiye da wadanda suka nuna musu goyon baya tun farko. A cewarsa, "Masana'antar mu ta ginu ne akan soyayyar masoya, amma abin takaici shine wasu daga cikinmu ba sa damuwa da mutanen gida. Sai dai su karkata ga wadanda ke waje, suna fifita su akan masoyan cikin gida."
Wannan kalami ya jawo cece-kuce da martani daga abokan aikin mawakin, musamman abokinsa na kusa, Sani Candy. Sani Candy ya fito fili ya soki wannan furuci, yana mai cewa zargin Garzali ba shi da tushe balle makama. A cewarsa, "Masoyan gida su ne ginshikin nasararmu, kuma ba gaskiya ba ne cewa muna watsi da su. Duk da haka, kowa yana da hanyarsa ta gudanar da aikinsa, kuma bai kamata a yi irin wannan sukar ba a fili."
ga videon kadan daga cikin abunda ya fadaSauran abokan aikin Garzali ma sun bayyana damuwarsu kan maganganun nasa, suna ganin cewa ya kamata a guji irin wannan kalami domin yana iya jawo rabuwar kai a masana'antar. Wasu daga cikinsu sun bukaci a samu fahimtar juna da sasanci tsakanin Garzali da abokan aikinsa domin ci gaba da hadin kai.
A yayin da wannan batu ke cigaba da jan hankali, masoya sun rarrabu kan lamarin. Wasu sun goyi bayan Garzali, suna cewa ya fadi gaskiyar da ya kamata a saurara, musamman ganin cewa wasu jarumai da mawaka suna watsi da masoyan gida. Wasu kuwa sun yi Allah-wadai da kalamansa, suna ganin ya yi tsaurin baki, kuma bai kamata ya furta haka ba a fili.
Duk da cece-kuce da suka biyo bayan maganganunsa, babu shakka wannan batu ya nuna muhimmancin masoya a rayuwar mawaka da jaruman masana'antar. Masoya su ne tushen daukakar jarumai, kuma yana da kyau su samu kulawa da girmamawa ba tare da la’akari da ko daga ina suke ba. Wannan ya zama darasi ga kowa, musamman mawaka, cewa alakar su da masoya na bukatar kyautatawa a ko da yaushe domin ci gaba da samun daukaka da nasara.


Comments
Post a Comment