Yanzu - Yanzu masu shirya film din Garwashi sun saka gasar da za'a samu manyan kyaututtuka
Kwararriyar marubuciya kuma shugaban kungiyar jin kai da taimakon marayu na kano hajiya Fauziyya D Sulaiman ta sanar da wani sabon gasar da suka sa musamman ga makallata shirin garwashi inda ta bayyana cewa
GASAR RUFAIDA YOGHURT TA GARWASHI SEARIES KASHI NA BIYU
Kamar yadda muka saba kawo muku gasa kala-kala domin amfanar masu kallon shirinmu Garwashi #garwashi, yanzu ma shararren kamfaninmu na Rufaida yoghurt ya zo muku da wata gasar wacce mutum goma da suka ci, za su amfana da kayan kamfanin Rufaida a kowacce Jaha suke, kuma zaa dinga yin wannan gasar duk karshen wata Insha Allah.
Gasar itace; wadannan hotunan na kasa da Ma'u ta je gidan Baba Lami da yaranta, shin waye zai iya fadar abun da ya kai Ma'u gidan Baba Lami da daddare? Wanda amsar tana cikin Garwashi S2. Ep8 na gobe Litinin da zai zo muku.
Wadanda suka canki amsar dai-dai za su samu kyautar kayan kamfanin Rufaida na Naira Dubu goma (10k) kome suke so a kamfanin, ko YOGHURT ko Beridi ko ruwa, gasar za ta fara daga yanzu zuwa gobe Litinin karfe Hudu na yamma.
Bisimillah a Kafta!!!
Ga hotunan da take magana akansu
Comments
Post a Comment