Tsohon Jami'in DSS Ya Karyata Jita-Jitar Kisan Abacha, Ya Ce Ciwon Zuciya Ne Ya Yi Sanadinsa
Tsohon Mataimakin Darakta a Hukumar DSS, Dennis Amachree, ya sake tayar da muhawara kan mutuwar tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, bayan ya bayyana cewa binciken da ya gudanar ya nuna ciwon zuciya ne ya yi sanadin mutuwarsa a shekarar 1998.
Amachree ya ce yayin bincikensa ya yi tambayoyi ga wasu mutanen da ke kusa da Abacha a lokacin, kuma bai samu wata hujja da ke nuna an kashe shi ko an ba shi guba ba. Wannan ikirari na zuwa ne sabanin jita-jitar da ta dade tana yawo cewa wasu mata ko abokan hamayya ne suka haddasa mutuwar tsohon shugaban.
Duk da haka, batun mutuwar Abacha na ci gaba da kasancewa daya daga cikin abubuwan da suka fi jawo ce-ce-ku-ce a tarihin siyasar Najeriya, inda mutane da dama ke da ra'ayoyi mabambanta kan abin da ya faru a ranar da ya rasu.
Shin kana ganin bayanin tsohon jami'in DSS zai kawo karshen ce-ce-ku-cen da aka shafe shekaru ana yi kan mutuwar Abacha, ko kuwa har yanzu akwai tambayoyin da ba a amsa ba? Ka bayyana ra'ayinka a sashin sharhi. :::

0 Comments