Tinubu Ya Bukaci Mazauna Abuja Su Rika Biyan Haraji da Kudin Filaye, Ya Ce Ci Gaban Birnin Na Bukatar Kudi

 

Tinubu Ya Bukaci Mazauna Abuja Su Rika Biyan Haraji da Kudin Filaye, Ya Ce Ci Gaban Birnin Na Bukatar Kudi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja da masu gudanar da harkokin kasuwanci da su rika biyan haraji, kudin filaye (ground rent) da sauran hakkokin gwamnati ba tare da bata lokaci ba.

A cewarsa, kudaden shiga da gwamnati ke tarawa su ne ginshikin aiwatar da ayyukan raya kasa da samar da muhimman ababen more rayuwa da jama'a ke amfana da su. Ya yi nuni da cewa ana ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan gine-gine da tituna a sassa daban-daban na Abuja, wadanda ke bukatar kudade domin kammalawa da kuma kula da su.

Sai dai kalaman shugaban sun jawo martani daga wasu 'yan Najeriya, inda wasu ke cewa gwamnati ya kamata ta kara tabbatar da cewa jama'a na ganin tasirin harajin da suke biya ta fuskar tsaro, walwala da ingantattun ayyukan gwamnati.

Shin kana ganin biyan haraji a kan lokaci zai taimaka wajen kara ci gaban Abuja da Najeriya baki daya, ko kuwa gwamnati ya kamata ta fara nuna karin gaskiya kan yadda ake kashe kudaden haraji? Ka bayyana ra'ayinka a sashin sharhi. 

Arewa Pulse



Post a Comment

0 Comments