Zuwan Sadiq Saleh Da Auta Waziri Ya Rage Tasirin Mawaki Hamisu Breaker Da Abdul D. One

Zuwan Sadiq Saleh Da Auta Waziri Ya Rage Tasirin Mawaki Hamisu Breaker Da Abdul D. One A duniyar wakokin soyayya na Hausa, sunayen mawaka irin su Hamisu Breaker da Abdul D. One sun jima suna karbe zukatan matasa da masoya a fadin Najeriya da ma kasashen waje. Wakokinsu sun yi tasiri sosai a cikin zuciyar mutane, inda kowane sabuwar waka daga gare su ke zama abin jira kamar an bada labari. A shekarun baya, da zarar Hamisu Breaker ko Abdul D. One sun fitar da waka, cikin kasa da wata guda sukan tara sama da 1 million views a YouTube — hakan ya zama ruwan dare a duniya kade-kaden Hausa. Sai dai kamar yadda rayuwa ke tafiya, komai na da lokacinsa, kuma hasken da ke fitowa daga sabbin fitattun mawaka irin su Sadiq Saleh da Auta Waziri ya fara dusashewa kan tsoffin taurari. Wadannan sabbin jarumai sun zo da wani sabon salo mai cike da natsuwa, hikima da kalaman da ke taba zuciya, musamman ga masoya da kuma masu son jin dadin zuci. Auta Waziri da Sadiq Saleh sun zama tamkar sabbi...