Zan sa ayi miki dukan tsiya - momee gombe da samha m inuwa
Jaruma samha inuwa tana daya daga cikin jaruman da masana’antar Kannywood ta kora a yan kwanakin nan akan wasu hotuna da kuma bidiyoyin da ta saki wanda wayan nan hotunan da bidiyoyin sun bayyana wasu bangare da ga tsaraicin ta wanda hakan ya jawo wa masana’antar zage zage da cin mutunci wanda wasu ma suka dinga cewa ai duk Kannywood ne ta koya musu duk abunda sukeyi.
Hakan ya fusata manyan shuwagabannin kannywood wanda suka yanke hukuncin korarta daga masana’antar gaba ki daya, sai dai mun gabatar da bincike mun tabbatar da cewa tabbas daman tun can akwai wata makarkashiya tsakanin ta da shigaban tace fina finai koma dai menene Allah shi ya barwa kan shi sani.
Sai kuma gashi a kwana kwanan nan wani bidiyon ta tareda jaruma momee gombe da kuma abubakar bashir mai shadda ya ke yawo inda cikin raha suke fada mata cewa idan ta sake yin bidiyo tana zage zage wallahi har inda take sai sunzo sun saka anyi mata dukan tsiya ko basu yi ba to zasu dauko hayan mutane daga gombe su jibge.
Hakan ya biyo bayan tun wata rigima da ta shiga tsakaninta ita da babbar kawarta auta wanda akafi sani da Maryam kk, wanda sukayi da zage zage da cin mutuncin juna gami da tona asirin juna akan wani saurayin su ko ince wani wanda yake kashe musu kudi mai suna KWANDI.
Kwandi dai yana daya daga cikin mutanen da suke daurewa jaruma samha m inuwa gindi wanda shi kadai yana iya kashe kudi sama da 500k a live din samha sai kuma daga baya samhar ta hango shi tareda Maryam kk wanda har happy valentines tayi masa Hakan ya fusata samha m inuwa wanda har ya jawo cece-kuce tsakanin su da zage zage.
To wannan dalilin ne yasa momee gombe da bashir mai shadda suka jawa samha m inuwa kunne akan kada ta sake zagin wani ko wata a social media kamar yadda zaku gani a bidiyin nan na kasa.
Kafun nan dan Allah kuyi supporting din mu wajen dannan wannan links din Hakan zai kara mana kwarin gwiwa kawo muku muhimman labarai👉: Dannan nan
Comments
Post a Comment