Wasu Jarumai Uku Da Zuwansu Saudiya Ya Bawa Mutane Mamaki
Media sai cece-kuce kuce ake tayi akan zuwan wasu jarumai kasa mai tsarki inda wasu dayawa daga cikin mutane suketa mamaki yadda cikin kankanin lokaci jaruman har sun samu damar zuwa kasa mai tsarki wanda dayawa daga cikin yan uwansu jarumai wayanda suka riga su shiga harkar basu samu wannan damar ba.
Na farko itace jaruma fidausi yahya
Wannan shine karanta na farko da fara zuwa kasa mai tsarki inda jama'a suke ta mamaki ganin yadda cikin karamin lokaci ta samu kudi har taje Kasar Saudiyya wanda kwata kwata ko shekara uku batayi ba da shigowa masana’antar. Har wasu suna tambayar shin a ina ta samu kudin da ta shiga harkar.
Na biyu shine Abdul gaya
Jama'a dayawa sunyi mamakin ganin yadda abdul gaya yaje kasa mai tsarki sai dai wasu suna cece-kucen cewa jaruma momee gombe ne ta biya masa sai dai wannan labarin bashida tushe bashida asali kawai magana ce, Abdul gaya yana daya daga cikin manyan content creators da suke samun mahaukacin kudi a social media wanda a kalla yana samun sama da milyan 3 a wata saboda haka ba abun mamaki bane dan ya iya biyan kudin zuwa umra
Na uku itace Momee gombe
Duk da ba wannan bane na farko jaruma momee gombe taje Saudiyya yafi sau a irga, amma duk da haka mutane suna mamaki da tambayar yadda aka yi jarumar take zuwa kasa mai tsarki musamman masu amfani da dandalin tiktok da sauran kafafen sada zumunta
Wannan ba abun mamaki bane gaskiya, momee gombe tana daya daga cikin jaruman da suke samun kudade daga kannywood da kuma sanaoin da take gudanarwa wanda a duk shekara tana samun kudin da zata iya kai mutane sama da 10 umarah, kuma tana da masoya wayanda zasu iya biya mata kudin zuwa umarah
Kannywood news
Comments
Post a Comment