Suwaiba: Sanadiyyar Fina-Finai Ta Fada Cikin Mugun Hali

 


Suwaiba: Sanadiyyar Fina-Finai Ta Fada Cikin Mugun Hali

Suwaiba yar asalin Jihar Gombe ce, budurwa mai kwazo da buri a rayuwa. Tun tana karama take sha’awar fitowa a fim, tana mafarkin wata rana za ta zama jaruma sananniya kamar irinsu Hadiza Gabon da Rahama Sadau. Duk wanda ya santa ya san yadda ta ke kaunar harkar fim fiye da komai.

A haka ne ta ci gaba da bibiyar shafukan yanar gizo, tana neman dama don cimma burinta. A cikin wannan yanayi ne ta hadu da wani mutum a Facebook mai amfani da sunan Yakubu Muhammad. A shafinsa, yana wallafa hotuna da bidiyoyin wasu fitattun jaruman Kannywood, yana rubuce-rubuce kamar wanda ke da kusanci da masana’antar. Bai dauki lokaci ba kafin ya fara janyo hankalin Suwaiba, yana bata fata da alkawuran da suka dace da mafarkinta.

"Idan kina so ki shigo cikin fina-finan Kannywood, ki samu shahara da kudi, ni zan taimaka miki. Ina da sanayya da manyan daraktoci kuma zan saka ki cikin wani sabon fim da ake shirin farawa. Amma sai dai ana bukatar wasu kudade don shirya abubuwan da suka dace."

A cikin rudani da farin ciki, Suwaiba ta yarda da shi. Ta fara tara kudi daga karamin sana'arta na siyar da atamfofi, amma hakan bai isa ba. A cikin gaggawa, ta dauki kudi daga adashin da take gudanarwa a unguwarsu, ta kuma sayar da wasu kadarori da iyayenta suka mutu suka bar mata. Dukkan kudaden nan ta tattara su ta aika wa wannan mayaudarin mai amfani da sunan Yakubu Muhammad.

Sai dai tun bayan da ya karbi kudin, abubuwa suka canza. Da farko, ya rika bata kwana-kwana da dalilan da suka hana fim din farawa. Daga baya kuma, sai ya daina daukar wayarta gaba daya. Ta tura masa sakonni babu amsa, ta kira shi sau da dama, amma shiru. Sai lokacin ne ta gane cewa ta fada hannun wani makaryaci mai damfarar 'yan mata.

Hankalinta ya tashi, zuciyarta ta karye. Wadanda suka ba ta adashin da ta ci sun fara nemanta don a biya su hakkinsu. Bata da abin biya, kuma babu inda za ta samu. Ta fada cikin wani hali na damuwa da bakin ciki, tana tunanin yadda burinta ya lalace, dukiyar iyayenta ta salwanta, da yadda mutuncinta zai zube idan mutane suka fahimci abinda ya faru.

Kamar yadda aka ce, bakin ciki na da lahani. Kwanaki ba su jima ba, sai Suwaiba ta fara fuskantar matsalar jiki. Daga farko tana jin kasala, daga bisani kuma ta fara rasa ikon motsa hannayenta da kafafunta. A karshe ta fada cikin ciwon mutuwar barin jiki—paralysis.

Yan uwanta sun zo sun gan ta, amma ba su tausaya mata ba. Sun dauka cewa abin da ya faru da ita hukunci ne daga Allah saboda yarda da tayi da mutum da bata sani ba. Sun ki daukar nauyin maganinta, sun bar ta tana fama da matsalarta ita kadai. Duk wanda ya san Suwaiba da farincikinta da burinta, yanzu yana ganinta a kwance cikin wahala, idanuwanta cike da hawaye da nadama.

"Da na sani...!" Ita kadai ke maimaita hakan a kowane lokaci, amma hakan bai canza komai ba. Mafarkinta ya zama mafarki mara tabbas, rayuwarta ta rushe gaba daya, kuma ta kasance cikin wani hali na bakin ciki da babu wanda ke son taimakonta.

Darasi

Labarin Suwaiba darasi ne ga duk wata yarinya da ke son shigowa harkar fim ko wani fannin rayuwa. Kafin a yarda da kowanne mutum a yanar gizo, dole ne a tabbatar da gaskiyarsa. Rashin hankali wajen daukar mataki na iya rusa rayuwa gaba daya.

Duk da halin da Suwaiba ta shiga, akwai fatan samun sauki. Idan har zata samu masu tausayawa da taimakonta, watakila zata iya samun kulawar likitoci ta samu lafiya. Amma idan babu wanda ya taimaka, to labarinta zai kasance cikin jerin labaran mata da suka tafka babban kuskure har ya zama sanadiyyar halakar rayuwarsu.

Allah ya kiyaye mana rayuwarmu daga sharrin makaryata da masu damfara.

Cikakken bidiyo



Comments