Sabuwar Fitina Ta Kunno Kai Tsakanin Rashida Mai Sa'a Da Sadiya Haruna

 

Daya daga cikin masu goyon bayan rashida mai sa'a ta futo ta baiwa uwar dakinta hakuri akan ta bari sai bayan sallah ayi rikicin tunda yanzu azumi ake.


Rigimar sadiya haruna da rashida mai sa'a tun ba yau ba aka soma shi kuma an dau lokaci anayi tun lokacin auren G fresh inda sadiya haruna take zargin rashida da cinye kudin anko na mutane.
Kuma tana zargin itace ta zuga alpha charles har aka fasa auren su da g fresh.

Wanda an kai ruwa rana kuma an jima ana cacar baki tsakanin jaruman wanda lamarin har ya kai ga tone tonen asiri inda alpha charles ta bayyana wa duniya cewa sayyada sadiya haruna tayi mata asiri har ta kwanta rashin lafiya.

Wannan lamarin dai yaki ci yaki cinyewa har akace za'a kai kara gun yan sanda.


Comments