Mummunar Kishi: Labarin Yarinyar da Kaddara Ta Shafa
Mummunar Kishi: Labarin Yarinyar da Kaddara Ta Shafa
Amina da Maryam sun taso tare kamar ‘yan uwan juna. Sun kasance abokan juna tun suna Ζ™anana, suna cin abinci tare, tafiya makaranta tare, da raba sirrika tsakaninsu. Maryam ce mafi kyawu a cikin su, kuma duk inda ta shiga mutane suna yabawa kyawunta. Sai dai wannan kyawu ne ya zama tushen fitinar da ta rushe komai a rayuwarsu.
Amina na da saurayi mai suna I, wanda suke da burin aure. Sai dai, lokaci ya wuce Maryam ta hadu da Sadiq, suka fara soyayya ba tare da sanin Amina ba. Da ta gano cewa abokiyar amincewarta tana soyayya da saurayinta, zuciyarta ta karye. Kishinta ya turnike, ya rufe mata ido, har ta yanke shawarar yin wani abu da ba zata taba tunanin zata aikata ba.
Amina ta nemi boka. Ta fada masa cewa tana son ya yi wa Maryam asiri kada ta taba yin aure a rayuwarta. Bokan ya yi dariya, sannan ya ba ta tabbacin cewa zai yi mata abin da ba za a iya juyawa ba. Bayan kwana uku, Maryam ta fara rashin lafiya. Da farko ciwon kai ne kawai, sai ciwon ciki, sai kuma ta fara ramewa. Duk likitoci sun ce ba su gane abin da ke damunta ba. A cikin watanni uku, Maryam ta yi rauni sosai har ta mutu.
Lokacin jana’iza, Amina ta ji tsoron halin da ta jefa kawarta. Amma ta share zuciyarta da tunanin cewa yanzu zata samu Sadiq ya aure ta. Sai dai rayuwa ba ta tafiya yadda ake so. Bayan shekaru biyar, Amina ta cika shekara 23, ta kusa yin aure da wani saurayi da ya girmi Sadiq. Amma sai ta fara mafarkai. Kowanne dare sai ta ga Maryam tana kuka tana kiranta. “Kin hallaka ni, Amina! Kin rusa rayuwata! Amma fa ba zaki zauna lafiya ba.”
Tana farkawa sai jikinta ya yi sanyi. Ta kasa bacci, ta kasa cin abinci. A karshe, ta koma wurin bokan da ya yi mata aiki a baya.
Bokan ya kalle ta, ya yi dariya mai cike da tsoro. Ya ce mata, “Iskokan da suka dauki Maryam sun dawo wurinki. Sun ce dole ki basu wani abu daga jikinki—nonon ki na hagu—ko kuma su jefa ki cikin bala’i.”
Amina ta girgiza kai da sauri. “Ba zan iya ba!”
“Idan ba ki bayar ba, sai ki gani,” in ji bokan.
Amina ta tafi gida cike da tsoro. Ta yi kokarin mantawa da maganar bokan. Auren ta ya kama. Ango ya dauke ta gida. Sai dai washegari da safe, tana tashi daga barci ta ji wani irin zafi a bangaren hagu na kirjinta. Ta kalli jikinta, sai ta ga nononta na hagu ya rube, yana fitar da wari da tsutsa!
Mijinta ya shiga firgici. Bai san me ke faruwa ba, amma ya san cewa ba zai iya zama da ita ba. Iyayensa sun yanke shawarar cewa dole ya sake ta.
Amina ta koma gida cikin bakin ciki, nadama da tsoron abin da zai biyo baya. Ta gane cewa rayuwa ba wasa ba ce, kuma duk wanda ya aikata sharri dole wata rana zai gamu da sakayyar sa.
“Kaddara tana da hanyarta ta biya duk wani hakkin da aka take.”
Comments
Post a Comment