Jaruman Kannywood 5 da suka ya mutsa hazo

 

Wayan nan su ne jaruman kannywood biyar da suka ya mutsa hazo a yan kwanakin nan nafarko shine jarumin adam a zango


Jarumi Adam a zango yana daya daga cikin jaruman da suka ya mutsa hazo a yan kwanakin nan wanda malamai sukai ta magana akan shi saboda wani bidiyon da yayi sanye da Alkyabba wanda su malaman a ganin su duk wanda ya saka Alkyabba yayi bidiyo musamman na Kannywood to yayi ridda.

Na biyu ita ce zahra diamond

Cikin yan kwanakin nan Zahra diamond ta fadi wasu abubuwa wanda hakan ya jawo muhawara da cece-kuce a social media, jarumar ta futo ta bayyanawa duniya ce duk masu kallon su (Hausa film) jahilai ne basu da cikakken hankali wannan maganar ya batawa jama'a dayawa rai kuma sunyi takaicin abunda ta futo ta fada wa duniya.

Na uku itace Fatima hussain.


Jaruma Fatima hussaini ta tada yamutsi kwanan nan bayan ta futo a wani film mai suna jamilun jidda inda ta futo a matsayin kirista hakan ya jawo manyan malamai sunyi ta tabka muhawara cikin su akwai dr bashir wanda yake ganin futowarta din a matsayin tayi ridda kuma dole ta sake karbar musulunci, sai dai prof. Makari yace wannan fatawar tashi batada tushe wanda har akai ta muhawara akan, wannan ma ya jawo cece-kuce sosai.

Na hudu itace hadiza gabon

Jaruma hadixa gabon ta jawo cece-kuce sosai tun bayan da masoyanta suka ganta ta canza kamanni ta canza daga yadda aka santa hakan ya jawo magana sosai wanda ya yamutsa hazo tsakanin jarumar da kuma masoyanta

Na biyar itace jaruma Firdausi Yahya.


Itama tana daya daga cikin jaruman da suka tayarda kura a Kannywood tun bayan da futo acikin film din jamilun jidda inda tayi ta kwaba da wasu kuskuren da turanci wanda hakan ya jawo cece-kuce da kuma maganganu a kafafen sada zumunta

Kalli abunda ake koyawa jarumar kannywood.



Comments