Ingantaccen maganin suga

 

Ingantaccen maganin ciwon suga


Wannan maganin ciwon suga ne sadidan indai zaku juri amfani dashi to wallahi zaku samu sauki daga ciwon suga insha Allahu

Akwai wata itaciya ko kuma gari da ake kira sakayau wasu suna kiranta da dalam wasu kuma suna kiranta da kashe zaki duk mai maganin gargajiya yasanta kuma ana jarrabata dan ganeta

In kaje gun mai sayarda garurruka ba gargajiya ka ce ya baka sakayau ko kashe zaki ko kuma dalam idan ya baka sai ka dandana shi kadan a bakin ka bayan yan wasu mintuna sai kasha suga zakaji baka jin dandanon sugar to wannan shine ake kira da sakayau

So wanna garin ana shan shi cikin cokali a shayi ko kunu amma amfi shanshi a kunu kuma karamin cokali ba babba kullum ake sha wallahi indai ciwon suga ne za'a dace

NB: Bamu da hakkin mallakar wannan rubutun, Dr isa shine mai wannan rubutun mun kawo muku ne dan ku amfana.

Comments