Hukumar tace fina-finai ta mika babban sako ga yan film kuma zata dauki tatstsauran Mataki
Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano Ta Hana Shigar Banza, Chakuduwar Maza Da Mata, Da Shaye-Shaye a Gidan Gala Lokacin Wasan Sallah
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta amince a gudanar da duk wani biki ko wasan gala da ke kunshe da shigar banza, cakuduwar maza da mata, ko shaye-shaye ba, musamman a lokacin shagulgulan Sallah.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugabannin hukumar, inda suka jaddada kudurinsu na tabbatar da cewa al'adun gargajiya da na addini suna ci gaba da zama ginshikin rayuwar al'ummar Kano. Hukumar ta ce tana da hurumin sa ido da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa duk wani biki ko taron nishadi ya gudana bisa ka'idojin da suka dace da al'adar yankin da kuma koyarwar addini.
A cewar hukumar, an fitar da wannan gargadi ne domin dakile tabarbarewar tarbiyya da kuma kare mutuncin al'umma, musamman matasa. Hukumar ta kara da cewa za ta sanya ido a dukkan wuraren da ake shirin gudanar da wasannin Sallah don tabbatar da an bi dokokin da aka shimfida.
A baya ma, irin wannan dokoki sun sha haifar da cece-kuce a tsakanin masu shirya fina-finai da mawaka, inda wasu ke ganin hakan wani yunkuri ne na takura wa masana’antar nishadi. Sai dai hukumar tace fina-finai ta Kano ta dage kan cewa wannan mataki yana da muhimmanci wajen kare al’adar yankin da kuma tabbatar da an kiyaye ka’idojin da suka dace da al’ummar Jihar.
Daga karshe, hukumar ta gargadi duk wanda ya saba wa wannan doka cewa za a dauki matakin hukunci a kansa. Hakan ya nuna cewa masu shirya bukukuwa da fina-finai a Kano dole ne su bi wannan umarni ko kuma su fuskanci hukunci daga hukumomin da abin ya shafa.


Comments
Post a Comment