Cin amana ko kare mutumci shamsiyya sadi da Tijjani gandu
Duk wanda yake masana’antar Kannywood yasan kusancin da ke tsakanin mawaki tijjani gandu da kuma mawakiya shamsiyya sadi, mawakan biyu suna tare tun kamun su samu daukaka sun shafe shekaru dayawa suna soyayya wanda har ya kai an fara tunanin aure amma sai dai daga baya aka fara samun korafe korafe da kananun maganganun tsakanin masoyan guda biyu inda ta bangaren shi tijjani gandu yake korafin ita shamsiyya sadi ta cika kishi da kuma zuciya.
Wanda duk wanda yasan shamsiyya sadi yasani cewa mutumiyar kirki ce kuma tanada kamun kai ta fito daga gidan mutunci sai dai gaskiya tanada zuciya da cakwaikwaiwa abu bai kai abu ba zakaga tayi magana akai, sannan kuma tanada kishi sosai sai dai kuma tana yin kishin ne dan saboda tana sanshi, kamar yadda ya bayyana bata taba san wani da namiji ba kamar yadda ta so Alhaji tijjani gandu.
Sai dai kuma daga bangarenta kwanakin baya anyi wata tattaunawa da ita inda take bayyana halin da ta shiga tun bayan rabuwa dashi wanda ta so shi tsakanin ta da Allah amma daga karshe yayi mata butulci, Kannywood news ta yi kokarin jin ta bakinta amma abun yaci tura sai dai wasu daga cikin makusantanta sun tabbatar mana da cewa;
Tun bayan da tijjani gandu ya samu daukaka kuma gwabnati ya dawo hannunsu ya chanza Dabi'u, shine biye biyen mata da kule kule mata acikin wayanda ma yake nema harda wata kawar shamsiyya sadin, hakan ya bakanta mata rai, kuma tun daga lokacin ta daina samun lokacin shi ko da ta kirashi sai yake nuna mata yana wani uzurin.
Bayan faruwar hakan da yan kwanaki sai aka hango mawakin da wata jarumar tiktok mai suna meenaluwa suna harkokin su tare wanda jama'a da dama suna zargin ko soyayya sukeyi hakan ya jawo aka fara gaskata maganar shamsiyya sadi inda mutane da dama suke ganin mawakin bai kyauta ba ko kadan kuma a irin labarin da ta bayar ya cutar da ita sosai.
Kamar yadda zaku ga bidiyon shi da jaruma meenaluwar a kasa, amma kafun nan muna rokon ku da ku danna links din nan wannan shine zai kara bamu kwarin gwiwa wajen kawo muku labarai masu inganci masu tushe: DANNA NAN DAN ALLAH
Comments
Post a Comment