Abin Takaici: A Wannan Zamanin, Ina Ganin Mata da Yawa Suna Sukar Juna Kawai don Burge Maza – Zara Diamond Ta Sake Kiran Ruwa
Abin Takaici: A Wannan Zamanin, Ina Ganin Mata da Yawa Suna Sukar Juna Kawai don Burge Maza – Zara Diamond Ta Sake Kiran Ruwa
Fitacciyar jaruma kuma mai gabatar da shirin podcast, Zara Diamond, ta sake jefa magana mai cike da tada hankali a sabon shirin su na podcast. A cikin shirin, ta bayyana cewa a yau mata da yawa suna bata lokacinsu wajen sukar juna da kuma yarda su shiga duk wani hali kawai don burge maza.
Zara Diamond ta yi tsokaci kan yadda wasu mata ke ganin cewa idan sun goyi bayan juna, ko suka gina junansu, hakan ba zai sa su burge maza ba. Saboda haka, sai su fifita cin mutuncin juna da bata sunan junansu a gaban maza don su sami karbuwa. A cewarta, wannan dabi’a tana hana mata ci gaba kuma tana raunana su a idon duniya.
A cikin shirin, ta jaddada cewa macen da ke yin abu kawai don burge namiji ba komai ba ce illa sokuwa. Ta bayyana cewa lokaci ya yi da mata za su fahimci cewa darajar su ba ta dogara da yadda maza ke kallonsu, sai dai yadda suka gina junansu da kuma yadda suka amince da kansu.
Wannan furuci nata ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke yaba mata bisa gaskiyar da ta faɗa, yayin da wasu kuma ke ganin cewa ta yi tsauri wajen yin furucin. Duk da haka, maganganunta na ƙarfafa mata su daina kallon kansu a matsayin masu dogaro da ra’ayin maza, kuma su fara goyon bayan junansu don gina rayuwarsu.
Mene ne Ra’ayinka?
Ko kana tare da Zara Diamond a kan wannan batu? Ko kuwa kana ganin cewa ta yi tsauri a maganarta? Fadin ra’ayinka yana da muhimmanci wajen cigaban wannan muhawara!
Ga hoton rubutun nata da tayi.
Comments
Post a Comment