Tirkashi Jarumi Garzali Miko Ya kira Ruwa



Furodusoshi da daraktoci kai dama sauran crew na Kannywood kowa sai tofa Albarkacin bakin sa yakeyi inda ko wannen su babu wanda ya nuna goyon baya ga jarumin sai dai yan uwanshi jarumai

Mawaki kuma jarumi garzali miko yayi korafi ne akan yadda ake tauye hakkin su lokacin sallama idan sun yi ma wani furodusan aiki.

Inda ya bayyana cewa yaji kishin kishin cewa an karawa crew kudin biya sai dai su jarumai har yanzu babu abunda aka kara musu kuma yace zasu kafa kungiya inda zasu yi bore akan abunda ake musu.

Sai dai dayawa daga cin daraktoci da kuma Furodusoshi sun mayar masa da martanin duk jarumin da yace zai ki yin aiki dan Ba'a bashi abunda ranshi yakeso ba to zasu nemi wasu sabbin jarumai tunda ba iya shi kadai bane a Kannywood.

Wannan maganar ya jawo muhawara tsakanin jarumai da kuma Furodusoshi inda suke ganin babu adalci ko kadan akan abunda ake musu suma Furodusoshin sun nuna cewa ai a yadda ma suke biyansu basa samun wata riba

Yanzu dai haka masana’antar ta dau zafi ana ta muhawara a dukkan bangarorin ga hoto da video abunda yafara janyo cece kucen da kuma martanin Furodusoshin.








Comments