Jaruma hadiza kabara ta ballo ruwa akan maganar da tayi jiya wanda ya jawo cece-kuce


An hango jaruma hadiza kabara tayi wasu maganganu A wani sabon bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta wanda hakan ya jawo cece-kuce tsakanin ta da wasu yan tiktok kai harda ma wasu jarumai yan uwanta irin su Rashida mai sa'a duk da ba'aji mai sa'a tayi magana ba, wasu ne daga cikin makusantanta suka futo suna mayarda martani akan maganar da hadiza kabara tayi. 

 Rikicin dai ya zo da wani salo ko wannen su yakasa kama suna amma kuma duniya ta san da wayanda ake rikicin, wanda bangaren hadiza kabara akwai jaruma mansura isah da kuma Ladidi tubless.

Bangaren jaruma Rashida mai sa'a kuma akwai wani shahararren dan tiktok da ake kira da daddylola sai kuma tsohuwar matar da g fresh yaso ya aura alpha charles Borno da sauran masu goya mata baya. Rigimar ya samo asali tun maganar da hadiza kabara tayi lokacin da take yiwa matar g fresh fada, inda take cewa "kada ki dauko halin yanzu lawahan can 'ma'ana yan wahalan can' da da ya debo zai aura Allah ya taimake shi bai aureta ba" karara ya bayyana da su alpha charles da kuma wayanda suka tsaya mata takeyi su Rashida mai sa'a kenan. Ga video a kasa.

Jama'a dayawa sun bayyana ra'ayin su akan wannan rigimar inda suke cewa tayu daman tun can akwai jikakkiya, wasu kuma sukace ai batayi da Rashida mai sa'a ba, wasu kuma sukace tun daga kan yadda tafiyar take babu alamar akwai jituwa tsakanin jaruman tunda basa hada hanya daya. 

Koma menene dai in har muka samu sabbin update zamu kawo muku

Comments