Abunda Muka Bankado Game da Jarumi Adam A. Zango

 

Jarumi Adam A. Zango yana daya daga cikin fitattun jaruman masana’antar Kannywood, wanda ya shahara ba kawai ta fuskar iya rawa, waka, da fim ba, har ma ta fuskar rayuwarsa mai daukar hankali. Sai dai kamar kowanne fitacce, rayuwar Adam A. Zango ta cika da labarai masu dadi da kuma rudani, musamman dangane da soyayyarsa, alakarshi da abokan sana’a, da kuma irin taimakon da yake bai wa jama’a. Jarumin yafi ko wanne jarumi a Kannywood farin jini musamman a wajen matan kannywood wanda wasu ke ganin yana yawan basu fuska har hakan yasa wasu daga cikin su suka raina shi. Yafi ko wanne jarumi yin soyayya da yan matan da ke cikin industry su. 

Soyayyar Adam A. Zango da Jaruman Kannywood

  1. Maryam Booth
    Adam A. Zango da Maryam Booth sun kasance cikin wata soyayya da ta dauki hankula a baya. Wannan soyayya ta yi zafi a lokacin shekarar 2010 zuwa 2012. Duk da cewa ba su kai ga aure ba, an ce sun rabu ne cikin fahimtar juna, amma hakan bai hana jama’a cigaba da tofa albarkacin bakinsu ba.

  1. Nafisat Abdullahi
    Soyayya ta sake hada Adam A. Zango da Nafisat Abdullahi a shekarar 2013. Wannan alaka ta yi matukar daukar hankali, kasancewar dukkansu fitattun jarumai ne a masana’antar. Sai dai kamar sauran soyayyar da ya taba yi, wannan ma ta wargaje ba tare da samun aure ba, kuma wasu rahotanni sun ce rashin jituwa ne ya kawo karshen soyayyar.

  1. Fati Washa
    Bayan rabuwarsa da Nafisat, Adam A. Zango ya shiga soyayya da Fati Washa, wata fitacciyar jaruma a Kannywood. Soyayyar su ta dauki hankali tsakanin 2014 zuwa 2016, amma itama soyayyar ta kare ba tare da cimma biyan bukata ba.

  1. Ummi Rahab
    Daga baya, Adam A. Zango ya shiga wata rigima da jaruma Ummi Rahab, wadda ita ma ta kasance daya daga cikin wadanda ya yi kokarin ya taimaka musu a masana’antar. Rahotanni sun bayyana cewa Adam ya nuna sha’awar auren Ummi Rahab, amma hakan bai samu ba, kuma hakan ya jawo cece-kuce sosai a masana’antar. Wannan rigima ta jawo rashin jituwa tsakanin su har aka ga sun rabu da rashin fahimtar juna.

  2. Sai kuma tsohuwar matarshi Maryam Ab Yola

Itama jarumace daga cikin Kannywood wanda ita kam har aure sunyi amma kaddara ya rabasu

Masoya da Makiyan Adam A. Zango a Masana’antar Kannywood

Adam A. Zango yana daga cikin jaruman da ke da masoya da makiya sosai a masana’antar. Masoyansa suna yaba masa da kwarewarsa a fagen waka da kuma yadda yake bunkasa fina-finai. Duk da haka, yana fama da wasu rashin jituwarsa da wasu abokan sana’a. Misali, akwai jita-jitar cewa wasu jaruman Kannywood ba sa jin dadin yadda yake daukar kansa da kuma irin fadin albarkacin bakinsa kan al’amuran masana’antar.

Taimakon Jama’a

Duk da yake akwai jita-jita da cece-kuce, Adam A. Zango yana daya daga cikin jaruman da suka shahara wajen taimaka wa jama’a. An ce ya taba daukar nauyin karatun yara masu yawa a makarantu, musamman wadanda iyayensu ba su da hali. Haka kuma, ya kasance yana tallafawa marasa galihu ta fuskar abinci, sutura, da sauran kayan masarufi.

Daga cikin manyan ayyukansa na taimako, an bayyana yadda ya gina rijiyoyin burtsatse a wasu kauyuka domin taimaka wa mutanen karkara wajen samun ruwan sha. Wannan matakin nasa ya ja masa kara da yabon jama’a, har wasu ke ganin ya cancanci kiran sa jagora mai kishin al’umma.


Comments