Innalillahi Dan Bello ya sake tona asirin Ganduje da Daya jawo cece-kuce.
Yau zan bayyana muku daya daga cikin sata mafi girma a Kano. Wannan shi ne labarin yadda Dala Inland Dry Port, aikin da aka ce mallakin jama’ar Kano aka sace ya juya zuwa arzikin wasu ’yan tsiraru, wato Ganduje da iyalansa.
A cikin statement ɗin bankin Dry Port, za ku ga suna ɗaya yana ta fitowa. Abubakar Sahabo Bawuro.
Kullum yana zuba kuɗi. Naira miliyan 10 yau. Miliyan 20 gobe. Miliyan 50 sati mai zuwaHar ma da miliyan 100 da 150 lokaci guda. Ba tare da wani dalilin kasuwanci ba. Ba tare da wani aikin Dry Port ba. Ba tare da wata sana’a a bayyane ba.
Wannan ba zakakurin dan kasuwa ba ne. Muƙaddamin mutum ne da ake yiwa Kano zagon kasa da shi.
Sannan an yi amfani da Kamfanin gini da ya koma hanyar satar kuɗin gwamnati. Na buɗe statement na wani kamfani:
Sahab-Solid Construction Services Ltd. Sahab, Sahabi daga Abubakar Sahabo Bawura, kuma Abin da na gani ya firgita ni. Wannan kamfani wanda aka bude shi a matsayin kamfanin gini yana karɓar kuɗaɗe daga asusun gwamnatin Kano kai tsaye: ₦118,900,000, ₦48,500,000, ₦21,000,000, ₦83,833,000, ₦3.324 billion (eh, biliyan!), ₦100,000,000 sau da dama, da ₦500,000,000 a sau ɗaya!
Sannan daga nan nan take ake tura wa: Abubakar Sahabo Bawuro, da ‘yan kwangilar Dry Port, da ma wasu Accounts da keda alaƙa da wannan satar. Wannan ba kamfanin gini bane. Wannan tasha ce ta satar kuɗi talakawan Kano. Daga na kuma Dry Port shi kansa ya koma hanyar wankiyar kuɗi. Saboda me? Saboda Dala Inland Dry Port bai fara aiki ba, kuma ba ya gudanar da ciniki, amma account din bankinsa yana tafiya kamar inji.
Bayan Bawuro ya zuba miliyan 20, daga ciki nan take za ka ga miliyan 20 ta fita zuwa wajen“dan kwangila”. Bayan Sahab-Solid ta karɓi kudin gwamnati, sai ka ga Dry Port ya biya kudin katanga, lantarki, gini, hanya, duka da kuɗaɗen da suka fara fitowa daga asusun gwamnatin Kano. Bari na sawwaka muku.
Kuɗin gwamnati → Sahab-Solid → Bawuro → Dry Port → Contractors. Wannan shine ABU’nda Amma tambaya ɗaya ta rage: Wane ne ke cin gajiyar wannan dry port din? Wane ne mallakin komai bayan an gama? To nan ne gaskiya ta fito fili. Na samu takardun CAC na Safari Textile Ltd, da Safari Petroleum Products Limited. Wato kamfanin atamfa da yaduka da kuma na harkar mai. Kamfani mai suna “textile atamfa”, amma ya shiga maganar Dry Port.
To ga sunayen directors:
1. Hafsatu Umar — matar Abdullahi Ganduje
2. Muhammad Umar Abdullahi — ɗan Ganduje 3. Fatima Umar Abdullahi — ɗiyar Ganduje
4. Umar Abdullahi Umar — ɗan gida.
5. Abubakar Bawuro — eh, shi ɗin nan da yake zuba miliyoyin Dry Port! Kun ga yadda labarin ya haɗu? Mutumin da ke zuba kuɗi: director ne a kamfanin iyalin Ganduje. Kamfanin iyalin Ganduje kuma: yana karɓar kuɗin da suke wucewa ta asusun Dry Port. Safari Textile ba shi da alaƙa da sufurin kaya. Amma yana da alaƙa da iyalin Ganduje.
Kano ce ta biya kuɗin kaso 20. Kano ce ta gina. Kano ce ta samar da komai. Amma fa’ida ta tafi gidan Gidan Ganduje. Saboda haka a kwament, ku rubuta, wani irin hukunci ne ya dace da Ganduje?

Comments
Post a Comment