Babu inda akaci mutuncin addini anan, hasalima korewa sukeyi da nuna cewa masuyin hakan da sunan addini kuskure ne

 


Korewa suke yi...


Idan kace anci mutuncin addini saboda an nuna irin wannan shigar da su Shekau suke yi, kenan ka yarda Shekau musulmi ne tunda irinta yake yi.


Acikin masu zagin wannan Film har da masu jiran Algaita' su yi sabuwar fassarar fina-finan India irin waɗanda ake nuna Musulmai ƴan táádda ne su je su biya kuɗi a tura musu su kalla, ba tare da sun yi ƙorafi ba. Saboda ba Hausawa ne acikin Film ɗin ba.



Film ake so ayi dole a nuna labari a yadda yake, kuma sanannen abu ne masu yin irin waɗannan ayyukan tada tarzomar irin wannan shigar suke yi kuma su ɗauki litattafai suna fassarar son rai, ko kuma fassarar wasu Magabata ƙungiyar.... 


Duk lalacewar Hausa Film zai yi wahala a ƙarshen film ɗin nan a nuna waɗannan ƴan tááddan sunyi nasara.


Babban lefin masu Film ɗin nan da suka yi shi a ƙasar Hausa suka saka Hausawa da Yaren Hausa. Amma banda haka da wasu ma ba za su san anyi ba.


Na tabbata Mashirya wannan Film ɗin korewa suke yi ba tabbatarwa suke yi ba__ Ya kamata ma a yaba musu ba a zage su ba.

Comments