Da addu'a tana aiki, ba za a ga mutane a asibiti ba -Inji Ibrahim Sadam
Matashin ya rubuta kamar haka:
Ba na musun cewa addu’a ibada ce. Abin da nake tambaya shi ne ingancinta wajen yin tasiri.
Ga waɗanda suke irin su FB Lukmanus ko Socrates da suke cewa, “Da asibitoci na aiki, da ba a ga mutane a maƙabarta ba” — mutuwa tabbatacciyar dabi’a ce ta halitta, ba gazawar asibiti ba. Asibitoci an ƙirƙire su ne don su magance cututtuka na gaske, kuma suna yin iya ƙoƙarinsu bisa hujja da shaida — shi ya sa dukkanmu muke zuwa can.
Kowa zai iya bayar da hujja mai ƙarfi kan adadin rayukan da aka ceci a asibitoci yau da kuma waɗanda aka tsawaita rayuwarsu. Muna gaggauta zuwa asibiti domin a tsawaita rayuwarmu. To me yasa ba kawai addu’a kuke yi domin warkar da ku, ta haka rayuwarku ta tsawaita? Za ku iya kuma bayar da hujja cewa addu’a ta ceci kuma ta tsawaita rayuka?
Amma ga waɗanda suke cewa “ta yi min aiki” — ba za a ɗauke ku da muhimmanci ba, domin kowa a kowace addini da yake bautar wani daban yana da irin wannan ikirari. Har ma da Indiyawa da suke bauta wa duwatsu da shanu suna bayar da irin wannan shaida. Shin hakan yana nufin addu’a ba ta dogara da addini ko imani? Na biyu kuma, babu wanda zai iya tabbatar da hakan ga wasu.
Ku yi addu’a domin ita ibada ce. Ladar ta tana wajen Allah.

Comments
Post a Comment