Jerin Jaruman masana'antar Kannywood sha biyar da aka fara gajiya da ganinsu.

JERIN JARUMAN MASANANTAR KANNYWOOD DA AKA FARA GAJIYA DA GANINSU… Da dama cikin makallatan fina finai ko shirye shirye masu dogon zango na kannywood na kokawa da yawan ganin fuskokin wadannan jaruman kusan cikin kowanne shiri na masana’antar, ana ganin ya kamata a rage haskasu don fito da wasu jaruman watakila wadancan zasuyi fin abinda wadanan keyi muddin aka basu dama. Ko a cikin shirin matan gida da mashiryin fina finai Abubakar Bashir Maishadda yace ya kashe kusan Miliyan 50 don yin shirin kusan duk jaruman suna ciki, haka yake a wasu jiga jigan shirye shiryen masanaantar kannywood. Na tambayi Guda daga cikin masu bibiyar harkokin masana’antar, kuma jarumi a masana’antar Dabo Daprof shin cigaba da bayyana fuskokin jaruman da aka saba gani zai kawo cigaba ga masana’antar? Shin hakan zai bata damar gogayya da sauran takwarorinta na duniya. Ga amsar daya bayar👉 Yace: hakan ba karamar koma baya zai haifar ba a masana’antar, kazalika zai rage yawan makallata fina finan a kafafa...