Bidiyon gaskiya batu akan musuluntar jarumi Thalapathy

bidiyon Thalapathy yana sallah da musulmai. 


Gaskiyar batu akan musuluntar jarumi  Thalapathy.

Tun bayan Bullar wani bidiyo na jarumin bollywood yankin Tamil Thalapathy Vijay a kafafen sada zumunta Al'ummar musulmai suke ta muhawara akan ko shin jarumin ya musulunta ne, hakan ya jawo cece-kuce da kuma maganganu da dama wanda wasu suke ta yadawa a kafafen sada zumunta.
Gaskiyar batun shine, jarumin ba musulunta yayi ba kuma shi ba musulmi bane, hasalima idan kuka ga bidiyon dake sama zaku fahimci cewa jarumin bai san yadda ake sallah ba kawai yana bin su ne.

Tun bayan da jarumin ya bayyana shigar shi siyasa yake yin wasu abubuwan domin neman mabiya da masu kada Kuri'a, ba iya musulmai yayi wa haka ba har yan addinin Hindu da sauran addinai dake India yana bi yana musu hidima, abunda jama'a suketa gani akan jarumin duka siyasa ce amma ba musulunta yayi ba

Gidan jaridar indiafilmmantra itace ta rawaito wannan bayanin, inda ta shaidawa duniya cewa jarumin fa bai musulunta ba kawai ya taya yan uwa musulmai murnar shan ruwa ne a matsayin sa na dan siyasa kuma daman ai shi dan siyasa na kowa ne.

A bayanin sa da yayi a wajen taron ya kara nuna amfanin hadin kai da kuma martabawa da girmama ko wanne addini

Daga karshe duk masu yada cewa jarumin ya musulunta karya sukeyi amma muna fatan hakan insha Allah.

#kannywoodnews

Comments