Ashe kashe shehin crypto akayi
Sunana Nasir Idris Mahuta ina zama a garin bali gidana na bayan makarantar adamu primary dake garin bali.
Ina sayen shanu daga nan taraba ina kai su yankin kudu, ina da shaguna guda uku a bali, daya na custmatic daya kuma na sayar da wayoyi (handset) sannan daya shagon aski.
Ni mawakin wakokin siyasane sannan ina yin dukkanin abinda ya shafi ginin gida wato building plan, building designing, contractor ko building consultancy,Ina bawa dan kasuwa kudi ya sayi kaya idan ya sayar ya bani kudina da kuma riba Sannan ina saye da sayarwar mashina ina kuma bada haya a dinga bani ballance duk sati.
Watarana a watan JANUARY cikin 2018 james ya zo har dakina ya same ni lokacin ina tare da yaran gidana HAMZA da SENIOR muna zaune, muna tattauna akan mashin din da zan saya musu sannan ina yi masu gargadi akan su dinga kula sosai kada su sake maimaita kuskuren da zai sanya na sake karbe mashin din saboda dama na taba saya masu mashin daga baya na zo na karbe saboda rashin biyan ballance.
Mun gama magana zamu fita sai na tafi nayi wanka saboda lokacin ne na dawo daga kasuwa.
Bayan na dawo wanka sai na tarar da james yazo, bayan mun gaisa sai yace mini don Allah yana so yayi magana dani tuntuni yana kiran wayana bana dauka, nace masa da wanne layin yake kirana haka? Yace mini da MTN nasa sai nace bani da MTN din sai zain yace ya aje layin tuntuni.
Yace mini shagonsa babu kaya har yana jin kunyar zaman shagon saboda mafi yawan magungunan da ake nema bashi dasu yana ganin kudi sai dai su wuce saboda rashin kaya.
Yace mini dama wani INYAMURI ne ke bashi magani daga ONITSHA kullum idan yayi ciniki sai ya tura masa kudin basu taba samun damuwa ba sai ranar da ya turo masa da TRAMADOL na million biyu sai yan DRUGS suka tare motar da ta dauko masu maganin a katsina Ala suna bincikawa suka ga TRAMADOL sai suka kama kayan da kyar suka bar direban ya wuce bayan an basu kudi.
Yace yaje har katsina Alan ya basu kudi amma sunki karba da kyar shima aka bar shi amma maganin a gabansa aka kona.
Yace bashi da kudi ballantana ya turawa mai kayan kudin da yake dashi ya sayi wani fili a wajen hakimi.
Yace mutumin yana ta damunsa da kira shi kuma baya dauka saboda hakama ya aje layinsa na ZAIN shi yasa naga bai kirani da layin ba.
Yace mini don Allah na taimaka masa da jari sai mu dinga raba ribar shi damuwarsa duk maganin da aka zo nema a samu a shagonsa.
Nace masa yazo a sa'a yanzu nake son fita na sayawa su HAMZA mashina biyu kuma gaskiya iya kudin da nake dasu kenan.
Yace mini nawa suke bani balance duk sati sai nace kowanne mashin suna ana bani 5,000 ne. Yace don Allah na basa kudin da zan saya mashin din shi yayi alkawari zai dinga bani 10k din duk sati kafin ya mayar mini da kudina.
Nace masa sai dai nan gaba na basa don kuwa na riga nayiwa su Hamza alkawari sai dai idan sune suka ce na bashi.
Har kasa ya durkusa ya roki su hamza don Allah su bari a basa cikin sati biyu kadai zai maido kudin sai a saya musu, da ya fadi haka sai suka yarda.
Da muka gama sasantawa sai na dauki kudi 500k cash na ba shi ya mini godiya ya tafi.
Ya dinga bani 10k duk sati har lokacin da ya maido mini kudina. Daga wannan lokacin muka saba da james sosai har ya zama na yarda dashi fiye da kowa a cikin yaran gidana.
Saboda na yarda da James babu bukatar da zaizo da ita ban yi masa ba koda bani da damar yi nakan nemi damar domin na kyautata masa. Ya samu kudi sosai sanadiyyar jarin da nake basa. Bani da wani buri illa naga James yaci gaba shiyasa duk lokacin da na basa kudi yayi kasuwanci shine yake yanke nawa zai bani riba wani lokacin nakan ce masa ya maido min kudina kawai ba sai ya bani komai ba.
Ban taba tunanin James zai mini butulci ya sanya a bata mini suna don kawai yana so ya cinye kudin da na ara masa.
Ban taba matsawa james akan kudin ba shi yasa duk uzurin da ya bani ina karba na sake basa Date.
Yardar da nayi masa takai hatta idan zanyi tafiya zan kai SHANU Enugu ko Ebonyi nakan bar babbar wayata a hannun james kuma naba shi izinin amsa kowanne kira.
Hatta PIN da Union Bank dina ya sani yakan iya yin transfer na kudi a account dina idan wayata na hannunsa sai na dawo ya fadamin.
Yau gashi maimakon ya zama mai taimakona sai ya zama mai zaluntata.
Yayi amfani da wayata wajen tura text din da bansan iyakar adadinsu ba.
James na zuwa ya karbi kudi cash a hannuna idan an kawo masa magani sai ya sayar sai ya maido mini da kudina ya kuma bani riba.
Wani lokacin ina kasuwa zai kirani yace an kawo masa kaya sannan ya turamin account number din customern nasa na tura masa kudi, irin wannan tasha faruwa ban san adadi ba amma zan iya tuna wasu daga ciki.
A cikin wanda zan iya tunawa sune : ranar 16/march/2018 ya turamin account din CHARLES ANI na tura masa N200,000. A 26/march/18 lokacin ina katsina ya taba kirana yace yana bukatar 500k a wajena an kawo masa magani nace masa kudin dake account dina bai kai haka ba zan tura masa 221,500 zan kuma turo Sola ya basa N278500 sai ya turomin account din OBIDIKWU PETER na tura masaN221, 500 na kuma sanya Sola ya kaima sa N208, 500 a shagon duk a ranar sai ya kirani yace SOLA fa N208500 ya basa saura 70,000 sai nace nace zan tura masa a account na sa da anjima. Da aka turomin kudi sai na turawa james 70,000 zuwa account nasa.
Washe gari 27/march/2018 ya sake kirana yace dani wani ya kawo masa PASSION Mai arha sosai yace yana bukatar N200,000 ya biya mai maganin ya turo account din TIWATOPE PHARMACY na turawa account din N200,000.
A 26/apr/2018 James ya sake turomin account din ONYIRO MOSES LIBERTY na tura masa N500,000.
A 28/may/2018 ya sake cewa na turawa INNOCENT EZEAKO N25000.
A ranar 01/Aug/2018 ya tua mini account din NEWOBODO CHUCWUKA na tura masa N53,000 a rarrabe wato N14000 farko N4000 na biyu sai N35,000 sannan ya sake tura mini account din ADEPOJU TAIWO na tura masa N35,000. Bayan kwana hudu ranar 04/Aug/2018 ya sake bukatar na turawa Wani mai suna CHUCKWU PETER N260,000 A 06/Sept/2018 ya sani na turawa NNAJI CONFIDENCE N33,000, ya kuma sanya a 14/Jan/2019 na turawa NMANDI PATRICK N22,000.
A 25/Jan/2019 ya turamin account din wani mai suna OGUCHUKWU OKOLI N39, 000 a 29/Jan/2019 ma yasa na turawa OGUCHUKWU OKOLI N16,000.
A 11/Fwb/2019 james yasa na tura N36,000 zuwa account dina wani mai suna OGU OLIVER UCHENNA.
A 20/FEB/2019 ya bukaci na tura N112,000 zuwa account din wani mai suna OGUELI FREDERICK.
Wadannan sune zan iya tunawa kuma ina da tabbacin duka idan an duba Bank statement nawa za'a same su duka sannan nakan sanya yaron gidana sola ya tura masa kudade a account nasa wanda ba zan iya tunawa ba sai dai idan an duba account din yaron gidana to za'a samu dukka record din.
Bayan haka James yana zuwa ya karbi kudi cash a wajena ba zan iya tuna duka ba amma wanda na tuna sune:
Watarana a May 2018 James ya zo ya same ni a majalissarmu muna zaune sai ya faka motarsa ya fito ya kirawo ni yace na shigo matar ,bayan na shiga motar muka je gidan man Njwai ya sanya mai muka wuce wajen masu gasa kaza har kasayamini kaza daya.
Muka wuce roundabout ya fita ya sayo mini fearless sannan yace mini don Allah na sake ba shi aron 700k zai je jalingo ya sayo magani.
Yace dama kanansa dake kaduna yayi mashi alkawari amma sai hanya hanya yake ma shi ya hannasa. Yace amma sani mamarsuce ta zuga kanan.
Har na tambaye sh ya za'ayi mamarka ta zuga kada a baka jari?
Yace mini duk da ita ta haifeshi amma wallahi ta tsanes shi bata sonshi kawai hakuri yake yi. Yace tana zargin shi ya ka kashe babbansa da maita yayi kudi shi yasa bata taba yarda ta shiga motar shi ba tunda ya saya.
Nace masa babu komai zan iya bashi bisa sharadin zai dinga bani 30k duk sati kafin ya gama biyana.
Nace ya bari Sola ya dawo kasuwa zan san kirasa idan kudin sun hadu.
Bayan kwana biyu na kira shi yazo har gida ya tarar ana yi mini aiki. Da na basa kudin ya tafi nima sai na tafi sayowa masu aiki abinci . Da na dawo na tarar ya sayawa ma'aikatana softdrinks kowa daidai har guda uku suka rage ni kuma ya bada fearless da kaza yace a aje mini.
10/Jan/2019 James ya kirani da daddare yace na basa aron 500k akwai wanda zai kawo masa magani da daddare, sai nace masa ya bari SOLA ya shigo gida zan karbi kudi a hannunsa sai na hada da nawa.
Tun kafin sola ya dawo james ya dinga kirana har na rufe wayata saboda ya dame ni da kira.
Da asussuba sai gashi sun zo har gidana da Abdu boka (yaron gidana) yace don Allah na ba shi 500k wani ma'aikacin DRUGS yanzu haka yana gidansa tun misalin karfe 3 na dare ya kawo mashi TRAMOL na 800k amma sun shirya dashi 500k. Yace jiya ya ba shi sachets 2 ya gwada ya ga ko mai kyaune, yace yana so ya sallame sa ya tafi.
Yace zai samu riba sosai a kayan na taimaka masa zai tura mini kudina a cikin sati uku kacal kuma zai bani ribar 100k sai na dauki 500k na bashi suka hau mashin suka tafi.
A may 2019 james ya kirawo ni da sassafe bai same ni ba sai ya kirawo lambar wayar yaron gina SOLA yace dashi don Allah yana son magana dani yazo gidana ya buga bamu bude ba kuma ya kira bamu daukaba, da sola ya fada mini haka sai na bude wayata nace ya fadawa da james ya kirawo ni.
Sai James ya kirawoni yana cewa ya baro don Allah na taimakesa sai nace ya aka yi kuma? Yace yana so mu hadu yanzu don Allah nace a ina yace nazo filinsa na kusa da General hospital da na zo sai ya bani takardun filinsa yace na rike na basa aron million 2 wannan customern nasa mai bashi magani yazo yanzun haka yana hotel yace koda ya basa kudinsa ko kuma ya sanya police su kama shi a kai shi Onitsha shi kuma baya son kowa ya sani sai nace maganar gaskiya ni yanzu bani da million biyu 500,000 kadai za'a iya samu shima na aje ne zan tafi kasuwa dasu. Sai james yace don Allah tunda yaga Barmo yana nan don Allah na sanya baki ya ara masa kafin ya fara sayen nono zai biyasa.
Nace dashi to bari naje gun Barmo din tukunna idan na rokesa ya yarda sai na kirawoka.
Naje na roki barmo ya amince sannan na kira james nace yazo ya karbi kudin sun cika da yazo na dauki kudi na basa a gaban Hamza da Mustapha wanda sun zo gidana ne don suyi mini aiki. Sannan mukayi Yarjejeniyar cikin sati biyu zai maido kudin idan ya sayar da filayensa.
Har sati biyu ya wuce james bai kawo mini kudina karshe BARMO da kansa yasha zuwa gun james din yace don Allah ya basa ko wani abune ya fara sayen nono.
Ina zaune a gida sai james ya kirani a waya yace yanzu haka yazo sayar da motarsa a jalingo don ya samu ya bawa Barmo ya fara sayen kaya amma ana taya motar million daya saboda haka ba zai iya sayarwa haka ba zai dawo da ita bali ya sayar sai nace masa babu komai.
Da Barmo ya matsa mini sai sayar da matsinana guda Hudu nayi na fara bashi 800k daga har na gama biyan barmo kudinsa james ba bani ko sisi ba. Da naje na sami james na koka masa sai yace zai dinga bani 40k a kowanne sati ribana kamar yadda muka saba idan na basa kudi har ya gama biyana.
Dana matsawa james da kira akan kudina sai ya daina daukar kirana.
Saboda James ya raina mini hankali ni da na bashi asalin kudi sai gashi yazo gidana da wani malami Mai suka ce wai na basu daki zasu buga mini kudi miliyan 20 sai in dauki nawa.
Nace masa nifa ba yaro bane, kudina kawai nake so bana son wani shirita.
Karshe ya dauki malamin ya kai shi garba chede.
A haka har aurena yazo james bai bani kudina ba ana washe gari daurin aurena sai james ya kirani yace yanzun haka suna garba chede Malamin nan ya buga musu kudi kuma masu gobe zai kawo mini kudina.
Washe gari ya kirawo ni yace yanzu haka suna jalingo shida matarsa yarsu bata da lafiya don haka ba zai sami zuwa ba amma zai bawa KALIF Motarsa ya kawo mini a dauki amaryata washe gari zai dawo.
Bayan kwana 4 da aurena na fita ina dawowa sai na hango James shida wani suna gina rami a kofar gidana sai na tsaya har suka gama suka tafi sai nazo na tone ramin na ga kananun kwalbar magani guda uku da wasu layu a cikinsu sai na farfasa kwalaben na kira james na tambayesa yana ina yace mini yana jalingo baisan na gansa ba.
Na kira yaron gidana na fada masa yace wallahi kafin james suzo sai da yace masa yazo gidana ya duba ina nan ko bana nan da yazo yaga bana nan ya kirawo james ya fada masa.
Bankai minti 30 da fasa kwalaben ba sai nan take naji zazzabi ya kamani daga nan na kama rashin lafiya kamar zan mutu.
Washe gari 17/7/2019 har misalin karfe 10 na dare wayata na hannunsa. Yazo ya same ni da rana yace gobe zaiyi sammakon shiga jalingo zaije ya karbo kudin filayensa da ya sayar don ya bani kudina, ya bukaci na Tura masa Union mobile bank yace nasa yayi expire.
Na basa wayar nace ya tura da kansa na fada masa ni bani da lafiya harma yaje ya hado mini magani a chemist nashi.
Sannan nace masa tun da safe nake kokarin naga nayi transaction amma na rasa abinda yake damun bankina yaki yi sai yace bari ya gwada da ya gwada yace baya yi. Sai yace bari ya gwada turamin 1.5 yaga ko zai shiga sai ya turo ya shiga sai yace yana ganin dole sai naje banki.
18/7/2019 ya kirani misalin karfe 12:30pm yace ya karbo kudin saboda haka yana so mu hadu a hanyar takum yana so ya bani kudin ya wuce takum sai nace masa yazo gidana mana ina kwance bani da lafiya.
Yace baya son matarsa tasan ya dawo shiyasa don Allah nazo nace masa bazan iya ba gaskiya.
Yanata kirana, yanata kirana bana dauka saboda banci ya dauke ni.
Misalin karfe 4 ya kirani na dauka yace don Allah nazo gun nace masa to ina zuwa sai na aika yaron gidana ABDU nace yaje ya karbar mini kudina inda james din yace mu hadu. Bayan kamar awa 1 sai naji sallamar yaron gidana na tashi na bude masa kofa sai nagansa da police da bindigogi suka ce mu tafi Station ana nemana.
Nace masu to su bari na fadawa matana ko in sanya riga saboda lokacin karamin wando da singilate ne a jikina amma suka hana.
Da muka isa station police ya tambaye ni na gane james? Nace masa kwarai kuwa abokina ne, yace akwai rikicin kudi tsakanin ku? Nace masa babu rikicin kudi a tsakaninmu amma akwai kudina 2m dake hannunsa ya bani 130k yaune ranar da yace zai bani kudin.
A lokacin na zaci james yana so police su sheda ya bani kudinane ban taba tunanin ya kawo ni kara bane.
Police yace Nas karya kake? James yace ka zo shagonsa kace ya dinga baka kudi zaka hadasa da kamfanin magani a Kasar waje tsawon shekara biyu kenan yanzun haka ya baka kudi 2.6 amma yaji shiru babu magani babu dalilinsa shi yasa yake kararka a nan.
Na kalli james nace James dagaske kaine ka fadi haka sai yayi shiru.
Nace da police kwata-kwata babu gaskiya a maganar nan, amma gani ga james ya rantse mini da Allah yace anyi haka, ina fadin haka sai kanansa Barrister yace mini satin james biyu kenan baya iya magana suna zargin nayi masa asirine.
Suka nuna mini takarda sukace bank statement din james ne sunyi extracting kudin da yake bani sun lissafa adadinsu yakai 2.6 nace masu gaskiyane james yasha tura kudi a account dina amma saboda abinda suke fada bane ga james din nan ku tambaye shi.
Da na bukaci sunana mini takardar na gani na karanta sai sukace doka batace a bani ba nace to ina so muje banki muyo statement na account dina nima in nuna masu kudin da na dinga turawa james da wanda yake sanyani na turawa customers nasa masu kawo masa magani sai sukace babu hali don tun kafin su shigar da karata sunje sun sanya anyi freezing na account dina. Da naji haka sai na yarda saboda ko kafin su kamani nayi kokarin yin transaction amma Baya yi.
Sai na ciro wayata daga aljihu da niyar na kirawo sheduna wanda suka san alakarmu da james sai police din ya karbe wayata yace ance kada a taba barinka kayi kira sai yace na tashi ya kaini cell ya kulle.
Washe gari da safe bayan na kwana a cell ya fito dani yace nazo ya tambaye ni, yace na fada masa gaskiya nace masa wallahi abinda na fada maka jiya gaskiyar kenan nace yaje ya tambayi mai Anguwar Chamba ai ya taba sasantamu da James akan kudin sai police din yayi Mini tsawa sannan ya mare ni yace kada na rainasa.
Nace masa ya taba ganin dan damfarar da zai yi damfara a gida inda aka sanshi ballantana ya damfari yaron gidansa ko abokinsa wanda suke tare koda yaushe??
Nace masa abinda na sani shine dan damfara baya taba yin damfara a inda aka san shi kuma idan ya damfari mutum sau daya baya taba dawowa. Taya james zai dinga bani kudi akan zan kawo masa magani ban kawo masa ba kuma bai daina bani kudi ba kuma bai fadawa kowa ba? Sannan nida sayarda magani ba sana'ata bane sana'ar James ce amma yace haka?
Nace da police din kaima kayi tunani mana! Nafi james kudi kuma ninema nake basa kudi yake kasuwanci tsawon lokaci taya kuma na rasa wanda zan cuta sai shi?
Iyayena masu kudine, sannan mai gidana Alhaji Babaji a garin nan babu mai kudinsa amma ban cuce shi ba sai james yaron gidana?
Police din yayi shiru yace mu tafi ya maidani cell, nace don Allah ya bani wayata na kira matana na fada mata inda nake saboda banga yaron gidana yazo ba amma police din yaki.
Kimanin karfe 12 sai yaran gidana da mai Anguwa suka zo Station sun sami labarin abinda yake faruwa saboda haka sun zo bada shedar abinda suka sani sai aka koresu akace nan ba kotu bane sannan aka maidani cell.
Bayan lokaci kadan aka fito dani naga James da kanansa Barrister, ina ji police din na fadawa Barrister ayi sauri ayi Transferring case dina zuwa jalingo kada DPO yazo yaga Nasir, idan ya ganshi zai bukaci magana da shi kuma zai gano duk shirinmu, yace yayi magana da OC LEGAL don haka za'a tafi dani CID jalingo. Nan take suka bawa police din kudi sukace zasu yi gaba ya taho dani kafin muzo zasu shirya komai.
Sai aka maidani cell, bayan lokaci kadan aka fitar dani police din yace na sanya hannu a wata takarda, na tsaya zan karanta ya mare ni yace nayi sauri nasa za'a wuce dani jalingo sai na sanya hanu muka wuce jalingo.
Akan hanya police din yake cewa idan anje na nemi barrister saboda wallahi an shirya mini abinda ba zan taba fitaba sai anyi da gaske.
Da muka isa jalingo ya kaini wani office na iske barrister da james da police guda daya sukace na zauna a kasa.
Police da ya kawoni a Bali ya tafi, su kuma su Barrister sunata magana da police din da turanci.
Sai barrister ya tambayeni ina jin turanci kuwa nace masa a'a alhalin ina ji.
Ina ji yana fada masa cewa ni Musulmine yana so ayi dealing nawa yana so ayi mini sharrin da za'a daure ni ta yadda ba zan taba komawa Bali ba ballantana nayi kokarin daukar mataki.
Yace masa iyayena masu kudine saboda haka idan suka daureni yana da tabbacin iyayena zasu sako kudi sosai.
Suka gama maganarsu suka kaini cell.
Kwana shida babu wanda yazo guna kuma kullum police din zai fitar dani ya tambaye ni na fada masa gaskiya sai yace ina batawa kaina lokacine kawai domin dole na yarda da abinda ake zargina in kuma ba hakaba wallahi zasu rubuta abinda sai nayi 23 years a prison.
Sannan lokacin bani da lafiya sosai idan na bukaci magani sai police din yace sai na amince kafin a kawo mini magani duk da yake na yanke jiki na fadi acikin cell har suma na dinga yi saboda tsananin rashin lafiya amma suka ki yarda nasha magani suka ce dole sai na amince. .
Washe gari ina cell sai james yazo aka kirawo ni nace ina son magana da shi shi kadai sai Sunday ya kaimu wani office mukayi magana yana tsaye yana jin mu.
Na tambayi James zai iya rantsewa da Bible cewa na taba cutar dashi?
Zaka iya rantsewa na taba karbar kudi a hannunka wanda ba nawa ba?
Sai yace mini nayi hakuri wallahi ba laifinsa bane mamar shi taji yana so ya sayar da motarsa sai ta tura shi wajen kanansa Barrister tace yaje ya same shi a Jalingo .
Da yaje sai kanansa ya sanya Sars suka kamashi suka shi a cell ya kwana daga nan ya tambaye shi mai yasa yake ta kokarin sayar da motarsa da filayensa sai yace masa Nas ne ke bina kudi ya kuma bashi labarin komai shine kanansa yace bai yarda ba shine ya shirya yadda aka kamani.
Yace mini tun satin da ya wuce suke tsara yadda za'a kamani yana so ya fada mini amma kanasa yake jin tsoro.
Yace shj bai ji dadin hakaba shi yasa tunda ake abin bai taba yin magana ba, daga nan ya dina bani hakuri.
A kwana na 7 kimanin karfe 12 na dare police din ya fitar dani daga cell ya sake cewa na amince ko zanyi taurin kai? Nace masa gaskiya ni abinda na sani keban, yace eh ya sani abinda yake so na fahimta shine, bani da mafita yanzu haka bani da wata shedar nunawa ballantana na fitar da kaina, wadanda nake cewa sune shedata dukkaninsu basu zo ba, sannan ance kada abani waya ballantana na kira wani.
Idan ina son fita dole na amince zan biya kudi sai su bani waya na kira iyayena.
Yace idan na sanya hannu a wata takarda zai bani waya yanzu nayi magana da matana da kuma mamana da kowa nake so kuma zai kawo mini magani da safe tun da yaga inata kyamar zazzabi. Sai nace masa ni ba zan sanya hannu ba gaskiya sai wani nawa yazo, nan sai ya tashi ya dauko wani babban ice ya dinga bugun gwiwowina yace sai na sanya hannu. Ganin bani lafiya gashi yana azabtar dani nace ya kawo na sanya hannu.
Da na sanya hannu yace da nayi haka da tuni na fita ai amma taurin kaina yasa nake shan wahala. Yace gobe zai kaini gaban ogansa idan ya tambaye ni nace masa nine na bada statement din da na sanya hannu idan ina so a bani Wayata kuma a bada belina nace masa to shikenan. Yace wallahi idan kuma na fada masa cewa bani na fada ba to dama dai na san mai gidansu ba zama yake ba to idan ya tafi sai yayi mini bugun da ko tsayawa ba zan iya ba.
Washe gari ya kaini gaban ogansa duk abinda ya tambaye ni sai nace eh.
Da an jima sai aka bani waya nayi waya da yayana na fada masa halin da nake ciki na kuma yi waya da matana.
Daganan ya sayo mini anti maleria da paracetamol nasha.
Yayana ya kira abokinsa wanda S. A ne na gwamnan jihar Taraba ya sheda masa abinda ke faruwa yace don Allah ya taimakesa yaje ya fito dani.
Ina cikin cell sai naji ana kirana da nafito na sami HON. ABDULLAHI ALABURAH sai muka gaisa ya kuma gabatar mini da kansa ya tambaye ni abinda nayi na fada masa komai yace to babu damuwa yanzu duk abinda za'ayi zamu yi domin ka fita tunda mamarku tanata kuka hankalin kowa ya tashi. Abin bakin cikinma duka yaushe akayi aurenka da za'a yi maka haka?
Zuwansa ne yayana ya tura masa million daya ya bawa su james a matsayin part payment da sharadin zan cika sauran kudin bayan wata uku.
Bayan da na dawo gida cikin halin rashin lafiya haka na likitana ya dinga zuwa yana kula dani har na samu sauki.
Da na sami sauki sai na kira yaran gidana gaba daya na tambaye su mai yasa sun san abinda yake tsakanin mu da james amma basu zo sun bada sheda ba? Suka dinga bani dalili suka nuna mini bayan an kamani james ya dinga yi masu barazana yana ce masu zai kulla masu sharri suma idan suka shiga case din kamar yadda ya kulla mini gashi nan ina kulle daga nan prison za'a kaini.
Da naji haka nacewa yaron gidana ya rakani jalingo muje wajen BARRISTER na fada masa komai. Da mukaje tasha domin mu hau mota sai muka hadu da james ya wuce nima muma muka wuce.
Bayan mun dawo jalingo washe gari sai naji wani abokina ya kirani yana ce min kanan James yanzu haka yazo shagona yana nemana ni da yaron gidana boka yana cewa sai ya kashe mu, yace yanzun haka da bai samu yaron gidanka ba ya kamo hanyar zuwa gidanka saboda haka ka kiyaye. Bamu jima da gama waya ba sai naji anata buga gate din gidana kamar za'a ture gate din ana zage-zage sai ya taka gate din ya deko ta sama yana dubani ni kuma ina labe ina kallonsa security ware da na sanya a katangar gidana ne ya hana shi tsallakowa.
Ganin baiji motsin kowa a gidan ba sai ya buta "I will kill you nas" ya tafi.
Sai naji makafcina ya kirani yana cewa na fito naga abinda yaron nan ya rubuta da na fito na gani sai kawai na kirawo police suka dauki hoton rubutun nima na dauka yanzu haka case din na kotu.
Ashe tun lokacin james ya turomin text inda yake tsoratar dani akan ya samu labarin nace zanje kotu neman hakkina ban karanta sakon ba saboda rashin shiga email nawa sai kwanannan na gani.
Abinda zan iya tunawa shine lokacin da nake kokarin zuwa kotu kuma james ya samu labari sai suka hanani sakat suka dinga turo police kofar gidana hatta ranar da zamu fara zaman farko a kotu ban samu zuwa ba saboda sun turo police sunje tasha suna nema. Basu daina yi mini barazana da police ba sai da naje na sami D. P. O na bali ya jawa policemen kunne akan amfani da su da ake yi don kokarin ganin an hanani neman hakkina.

Comments
Post a Comment